Yadda ake kosan biredi da kwai

Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Mata da dama akwai hanyoyi da suke bi wajen yin kosai. Sai dai yadda wata za ta sarrafa nata kosan daban yake da yadda wata za ta sarrafa nata kosan. Wasu bayan sun markada waken sai su fasa kwai a ciki sannan su […]

Yadda ake kosan biredi da kwai

Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Mata da dama akwai hanyoyi da suke bi wajen yin kosai. Sai dai yadda wata za ta sarrafa nata kosan daban yake da yadda wata za ta sarrafa nata kosan. Wasu bayan sun markada waken sai su fasa kwai a ciki sannan su soya. Kamar yadda nake ba da shawara a baya cewa yana da kyau a koyi nau’ukan girki domin sanya kunnen maigida motsi akodayaushe. A yau na kawo muku yadda ake girka kosan biredi da kwai. A sha karatu lafiya.

Abubuwan da ake bukata:

•        Garin biredi

•        kwai

•        Attarugu

•        Magi

•        Kori

•        Garin tafarnuwa

 

HAdI

A samu biredi sannan a guggutsura shi kanana har sai ya bushe sannan a mutsuttsuka shi da hannu a saui garin. Ko kuma za a iya sayan garin biredi a manyan shagunan da ke sayar da kayan abincin zamani. A fasa kwai kamar biyar a ciki sannan a zuba magi. A jajjaga attarugu da tafarnuwa a zuba da kori. Sannan a kwaba sosai.

A samu tukunyar tuya a dora a kan wuta a zuba man gyada da albasa. Bayan ya yi zafi sai a sa cokali a rika gutsura kullun kamar yadda ake gutsura  kullun kosan wake ana zubawa a cikin man gyadan. Idan dayan gefen ya soyu sannan a sake juyawa zuwa dayan gefen domin ya soyu.  sannan a sauke.

Za a iya cin wannan irin kosan da kunu ko kuma shayi da safe ko a duk lokacin da ake bukata. A ci dadi lafiya.