Yadda ake kunun shinkafa da madara
Assalamu alaikum Uwargida. Yaya sanyi? Tare da fatar ana girka wa manyan gobe girkin da zai kara musu lafiya da kuzari. A yau na kawo muku yadda ake girka shinkafa mai madara. Kasancewar ana yawan rage abinci musamman ma idan farar shinkafa ce, wani lokaci ana rasa yadda za a yi da ita. Hakan ya […]
Assalamu alaikum Uwargida. Yaya sanyi? Tare da fatar ana girka wa manyan gobe girkin da zai kara musu lafiya da kuzari. A yau na kawo muku yadda ake girka shinkafa mai madara. Kasancewar ana yawan rage abinci musamman ma idan farar shinkafa ce, wani lokaci ana rasa yadda za a yi da ita. Hakan ya sanya a yau na kawo muku wani salon sarrafa wannan ragowar shinkafar. A sha karatu lafiya. Shan wannan kunun na rage wa manyan gobe yin mura a wannan yanayin sanyi.
Abubuwan da za a bukata
• Dafaffiyar shinkafa fara
• Madara
• Citta karama kwaya daya
• Sukari
• Kwayar tafarnuwa daya
• Ruwa
Hadi
A kankare danyar citta sannan a jajjaga ta a zuba ruwa a tace a ajiye a gefe. Sannan a bare tafarnuwa kwaya daya a jajjaga a zuba ruwa a tace. Sannan a hada ruwan tafarnuwar da na cittar a waje daya.
A tafasa shinkafa har sai ta yi laushi, sannan a debo garin madara daidai wadata a zuba a cikin ruwan cittar da tafarnuwar sannan a gauraya.
A zuba ruwan madarar a cikin shinkafar sannan a dora a kan wuta. Idan kunun ya fara kauri sannan a zuba sukari yadda ake bukata sai a sauke.
Za a iya shan wannan hadin da soyayyiyar ayaba ko zuma da kosai ko ’ya’yan itatuwa. A sha dadi lafiya!