Yadda ake kwalliya da ganyen ‘aloe vera’

Mata da dama na sha’awar ganin fatarsu ta yi sumul babu kuraje. Wannan ganyen na dauke ne da sinadarai da dama wadanda sukan iya dada tsawon gashin mace da sanya fuska sheki da gyaran jiki da dai sauransu. Son haka ne a yau na kawo muku hanyoyin da za a bi domin amfani da ganyen […]

Yadda ake kwalliya da ganyen ‘aloe vera’

Mata da dama na sha’awar ganin fatarsu ta yi sumul babu kuraje. Wannan ganyen na dauke ne da sinadarai da dama wadanda sukan iya dada tsawon gashin mace da sanya fuska sheki da gyaran jiki da dai sauransu. Son haka ne a yau na kawo muku hanyoyin da za a bi domin amfani da ganyen wajen gyaran fata da kuma gashin kai. Ina so masu karatu su gane cewa a duk rubutun da nake yi, idan na lissafo ababen hadin kwalliya, guda daya daga ciki nake so a rika amfani dashi. Domin yawan sanya wa fuska ababe da dama na haifar da fesowar kuraje.

• Kodewar fuska; yawan aiki ko shiga rana na sanya fuska ta yi baka ko kuma launinta ya zama biyu. A sami ganyen ‘aloe bera’ sannan a matse ruwan sai a matsa ruwan lemun tsami sannan a kwaba a rika shafawa a fuska domin gyaran irin wannan fatar.

• Yankwashewar fata; wannan ganye na rage shekaru daga fuskar mutum. A matso ruwan sa sannan a hada da ruwar ‘rose’ sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti goma zuwa goma sha biyar kafin a wanke a kullum.

• Domin fuska mai yawan gumi/maiko; a sami ganyen sai a dan kankare bayansa sannan a daura a tukunya da ruwa har sai ya yi laushi sannan a sauke a zuba zuma bayan ya huce sannan a shafa a fuska na tsawon minti 20 a kullum kafin a shiga wanka.

• Domin gautsin fata; a markada dabino da gurji sannan a matsa ruwan ganyen ‘aloe bera’ da ruwan lemun tsami sannan a shafa a fuska da jiki na tsawon minti talatin kafin a wanke.

• Gyaran gashi; a matse ruwan ‘aloe bera’ sannan a hada da man zaitun a kwaba su kwabu sosai sannan a rika shafawa a fatar kai da kuma saman gashin a duk lokacin da aka yi niyyar wanke gashin kai kafin a wanke . yin hakan na sanya bakin gashi da kuma dada ma gashin tsawo da karfi.