Yadda ake kwalliyar fuska
Mata da dama musamman ma wadanda za su yi aure sukan biya kudi mai yawa domin a yi musu kwalliyar fuska. Ba shakka daga an ga wanda aka yi wa wannan kwalliya lallai za a ce kwalliya ta biya kudin sabulu. Ina so in sanar da ku cewa wannan kwalliyanr za a iya yin ta […]
Mata da dama musamman ma wadanda za su yi aure sukan biya kudi mai yawa domin a yi musu kwalliyar fuska. Ba shakka daga an ga wanda aka yi wa wannan kwalliya lallai za a ce kwalliya ta biya kudin sabulu. Ina so in sanar da ku cewa wannan kwalliyanr za a iya yin ta a gida idan akwai kayan aiki.
•Da farko dai ana so a wanke fuskar da sabulu sannan a jira ta bushe kafin a shafa mata komai.
•Ana so a samu ruwan goge fuska (cleanser) a goge fuskar da shi da auduga.
•Bayan an yi hakan, sai a shafa man SPF (sun protection fuemula).
•A samu hodar fandesho dai-dai kalar fatar mutum sannan a shafa.
•A samu hoda haka a sake shafawa.
•Sannan sai a samu reza ga wanda ke da cikan gira sai a aske shi kadan.
•A samu gazal din mac guda biyu; daya baki daya kuma ba baki sosai ba sannan a zana girar da shi.
•Bayan haka sai a samu ‘concealer’ da na ‘eye shadow’ da burushin ‘eco tools’ da burushin ‘eyeliner’.
•Sai a fara taje giran da burushin ‘eyeliner’
•Sannan sai a zana girar da gazal din mac da dayan mara baki sosai a hada su.
•Bayan an shafa sai a sake taje su da ‘eyeliner brush’ din.
•Sai a dauko ‘brush sigma E65’ a debi eye shadow mai duhu a sake shafawa a girar.
•A sake dauko gazal din a sake zana giran sama da kasa.
•A shafa ‘concealer’ din da ‘brush E65’ din dai-dai kalar fatar mutum.
•Sannan sai a shafa ‘eye shadow’ kalar kayan da za a saka.
•Sai a shafa jan baki.