Yadda ake kwalliyar fuska 1
Mata da dama musamman ma wadanda za su yi aure sukan biya kudi da dama domin ayi musu kwalliyar fuska. Wasu su kan kashe naira dubu ashirin wasu kuma dubu goma don su samu suyi irin wadannan kwalliya. Ba shakka daga anga wanda akayi wa wannan kwalliya lallai za a ce kwalliya ta biya kudin […]
Mata da dama musamman ma wadanda za su yi aure sukan biya kudi da dama domin ayi musu kwalliyar fuska. Wasu su kan kashe naira dubu ashirin wasu kuma dubu goma don su samu suyi irin wadannan kwalliya. Ba shakka daga anga wanda akayi wa wannan kwalliya lallai za a ce kwalliya ta biya kudin sabulu. Ina so na sanar da ku cewa wadannan kwalliyar za a iya yinsu a gida idan akwai kayan aiki.
• Da farko dai ana so a wanke fuskar da sabulu sannan a jira ya bushe kamin a shafa mata komai.
• Ana so a sami ruwan goge fuska (cleanser) a goge fuskar da shi da auduga.
• Bayan anyi hakan, sai a shafa man SPF (sun protection fuemula).
• A sami hodar fandesho dai-dai kalar fatar mutum sannan a shafa.
• A sami hoda haka a sake shafawa.
• Sannan sai a sami reza ga wanda keda cikan gira sai a askesu kadan.
• A sami gazal din mac guda biyu; daya baki daya kuma ba baki sosai ba sannan a zana giran da shi.
• Bayan haka sai a sami ‘concealer’ da na ‘eye shadow’ da brush din ‘eco tools’ da brush din ‘eyeliner’.
• Sai a fara taje giran da brush din ‘eyeliner’
• Sannan sai a zana giran da gazal din mac da dayan mara baki sosai a hadasu.
• Bayan an shafa sai a sake tajesu da ‘eyeliner brush’ din.
• Sai a dauko ‘brush sigma E65’ a debi eye shadow mai duhu a sake shafawa a giran.
• A sake dauko gazal din a sake zana giran sama da kasa.
• A shafa ‘concealer’ din da ‘brush E65’ din dai-dai kalar fatar mutum.
• Sannan sai a shafa ‘eye shadow’ kalar kayan da za a saka.
• Sai a shafa jan baki.