Yadda ake lemon ’ya’yan kuka
Yadda ake lemon ’ya’yan kuka
’Ya’yan kuka na dauke da sinadarai kamar su Vitamin C, Calcium da Iron da Potassium da kuma Magnesium, masu muhimmanci ga lafiyar jiki.
Daga cikin abubuwan da ’ya’yan kuka suke kara wa jikin dan Adam, akwai:
⁃ Kara lafiyar zuciya
⁃ Taimakawa wajen narka abinci
⁃ Kara lafiyar fata
⁃ Rage kiba
⁃ Kara lafiyar kashi
⁃ Yana kara lafiyar hanta.
Kayan hadi
⁃ Kwalba
⁃ Madara
⁃ Abarba
⁃ Sukari
⁃ Ruwa
Yadda ake hadawa
⁃ A zuba ’ya’yan kuka a cikin roba sai a dafa ruwa na minti 30.
⁃ Idan ya jiku, sai a wanke hannu sai a kwaba sosai a cire ’ya’yan a tace.
⁃ A zuba madara a ciki, sannan a markada abarba a tace a zuba a ciki.
⁃ Daga nan sai a zuba sukari daidai yadda ake so a juye sosai ya hadu.
⁃ Sai a zuba a gora, a sanya a firinji ya yi sanyi sosai.
⁃ Ana iya sha da kankara.
Idan ba mai son madara ba ne, sai a zuba lemon abarba da sukari kawai.
Shi ke nan sai sha.