Yadda ake magance kumburin idanu
Ido yana daya daga cikin abubuwan da ake fara gani a fuska.
Kumburin idanu na faruwa ne a lokacin da idanun suka fara kumburi sakamakon yawan kuka ko yawan amfani da idon wajen karatu ko aiki a kan na’urar kwamfuta.
Wadansu kuma kumburin idanunsu na da alaka da wani canji da aka samu a jiki ko don yanayi walau kura ko rana.
Wadansu kuma nasu na faruwa ne saboda rashin barci ko kuma cin abincin da ba ya dauke da sinadaran gyaran ido.
Ido yana daya daga cikin abubuwan da ake fara gani a fuska don haka ya kamata mu kula da idanuwanmu.
Akwai hanyoyi da dama da suka kamata a bi don magance wadannan matsaloli na kumburin ido kamar haka;
• Shan ruwa hanya ce mafi sauki wajen magance kumburin ido domin, ruwa yana wanke daudar a ido.
Yawan shan ruwa yana da kyau a sha ruwa akalla kofi takwas zuwa goma a rana. Sannan kuma yana da kyau a rage cin gishiri.
• A samu cokulan karfe kamar biyar zuwa shida a saka a firiji na tsawon minti 10 zuwa 15 sannan a cire su, sai a rika shafawa a kumburin ido har sai ido ya sabe.
• Ganyen shayi yana magance kumburin ido: A jika ganyen shayi a ruwan dumi, sannan a cire a bari ya huce.
Sannan a kwanta a dora jikakkiyar jakar ganyen shayin a kan idanu sai a rufe idanu da kyalle mai tsabta.
A bari ya tsaya a hakan na tsawon minti biyar zuwa goma sannan a cire.
• Wata hanyar magance kumburin ido ita ce: A samu gurji a yanka sannan a saka a firiji na tsawon minti goma sannan a cire a dora a kan idanuwan har sai sun huce.