Yadda ake masa
Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya. Akwai hanyoyi da dama wadanda ake bi don yin masa. Yadda wata zata tsara na ta masar daban take da yadda wata uwargidan za ta sarrafa na ta. Akwai nau’ukan masa da dama kamar masar Gero da Dawa da Semo da kuma Shinkafa da […]
Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya. Akwai hanyoyi da dama wadanda ake bi don yin masa. Yadda wata zata tsara na ta masar daban take da yadda wata uwargidan za ta sarrafa na ta. Akwai nau’ukan masa da dama kamar masar Gero da Dawa da Semo da kuma Shinkafa da dai makamantansu. A yau na kawo muku yadda ake masar Shinkafa a cikin hanya mai sauki ba tare da an bada ayi ko kuma a saya ba.
Ababen da ake bukata
• danyen shinkafa
• Albasa
• Man gyada
• Yis da ‘baking powder’
• Siga
• Albasa
Hadi
A jika danyar shinkafa na tsawon awa daya sannan a wanke ta carak a zuba a cikin na’uran markade. Sannan a tafasa shinkafar kadan kafin ta nuna sosai sai a sauke a zuba a cikin wannan danyar shinkafar sannan a yayyanka albasa a kai sannan a markada har sai shinkafar ta yi laushi sosai sannan a zuba a cikin roba.
Bayan haka, sai a zuba yis a ruwan dumi kadan sannan a zuba a ciki. A sake dauko ‘baking powder’ a zuba a gauraya sosai sannan a rufe a sanya a rana har sai hadin ya tashi.
Sannan a dauko Tanda a daura a kan wuta. A zuba siga a roba da ruwa kadan yadda za ta narke sannan a zuba a kullun masar a sake gaurayawa . sannan a zuba man gyada kadan idan ya yi zafi sannan a debo kullun a zuba a ramukan tandar. Idan ya dan nuna sannan a sake juya masar zuwa dayan gefen domin ta nuna. Bayan ta nuna sannan a sauke a sanya a kwano.
Za a iya cin wannan masar ko waina da yajin kuli ko miyar taushe ko kuma miyar Alayyahu. A ci dadi lafiya.