Yadda ake miyar dage-dage
Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan alheri. Miyar dage-dage miya ce wadda ake yinta a tsanake. Ba miya ce wadda za a debo sauri a yi ta sannan a sanya tsammanin ta yi dadi ba. Yadda wata za ta yi nata miyar daban yake ga yadda wata za ta sarrafa miyar dage-dagen. Sannan akwai kura-kurai […]
Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan alheri. Miyar dage-dage miya ce wadda ake yinta a tsanake. Ba miya ce wadda za a debo sauri a yi ta sannan a sanya tsammanin ta yi dadi ba. Yadda wata za ta yi nata miyar daban yake ga yadda wata za ta sarrafa miyar dage-dagen. Sannan akwai kura-kurai da mata ke tafkawa wajen sarrafa wannan miyar. Idan lokacin bikin Sallah ya yi nan ne fa za a ga irin miyar da ake kawowa daga makwafta. Wata miyar ko dandanawa ba za a iya yi ba, saboda tsabagen tsami da kuma danyenta. Don haka ne a yau na kawo muku yadda za a sarrafa wannan miyar a tsanake.
Abubuwan da za a bukata
• Tumatir manya 10
•Tattasai kanana hudu
• Attarugu 5
• Albasa karama daya
• Ganda
• Kaza
• Nama
• Kori
• Tafarnuwa
• Man gyada ko man ja
Hadi
Da farko za a wanke wannan kayan miyar da na lissafo sannan a markadata. Daga nan sai a wanke kaza da nama da ganda a silalasu, har sai sun yi laushi. Sai a ajiye a gefe. A dora markaden kayan miya a wuta ya yi ta tafasa har sai ruwan ya tsane. Sannan a zuba man gyada ko man ja a yi ta soyawa, har sai man gyadan ya hauro saman kayan miya. Sai a dauko romon nama a zuba tare da naman a gauraya.
A zuba su magi da kori da kuma garin tafarnuwa, sannan a sake gaurayawa. A rufe na tsawon mintuna biyu, sai a dandana a ji in da tsami. Idan da tsami sai a jika kanwa kadan sosai a ruwa sannan a zuba kamar murfin kwankwalatin Fanta sannan a gauraya idan miyar ta nuna sai a sauke a ci da farar shinkafa.