Yadda ake miyar dargaza

Assalamu alaikum uwargida. Tare da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin miyar dargaza. Wannan miyar dai miyar al’ada ce ta mutanen Tangale da ke Jihar Gombe. Wannan miyar ita ake yi wa amarya a gidanta kafin ta fara kowane irin girki. Yana da kyau uwargida ta koyi girke-girke […]

Yadda ake miyar dargaza

Assalamu alaikum uwargida. Tare da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin miyar dargaza. Wannan miyar dai miyar al’ada ce ta mutanen Tangale da ke Jihar Gombe. Wannan miyar ita ake yi wa amarya a gidanta kafin ta fara kowane irin girki. Yana da kyau uwargida ta koyi girke-girke na al’adu da dama domin kwarewa wajen sarrafa girki.

Abubuwan da za a bukata

•        Itacen dargaza

•        Daddawa

•        Nikakkiyar gyada

•        Kifi (dubu a miya)

•        Magi

•        Attarugu

Da farko dai za a saro dargazar sannan a jika ta har sai ta fara yin yauki sannan a dora ruwa a tukunya sai a jefa daddawa da nikakkiyar gyada da jajjagen attarugu su yi ta tafasa har sai gyadar ta nuna sannan a zuba soyayyen kifin (dubu a miya) da magi a ciki a gauraya sai a dauko dargazar a zuba a cikin hadin miyar a gauraya sannan a rufe na tsawon minti biyar sannan a sauke.

Wannan miyar dai an fi hada ta da tuwon dawa kuma ana iya hada ta da kowane irin nau’in tuwo da mutum ke sha’awar cinsa.