Yadda ake miyar kuka da man shanu
Barkanmu da warhaka uwargida. Ko kun san cewa miyar kuka hadaddiyar miya ce kuwa? Mutanen karkara da dama sun tsane ta ko kun san dalilinsu? Babu wani dalili illa ba su san yadda za su sarrafata ba ce. Kuka miya ce ta babban gida, inji masu magana suka ce “Kuka hana kukan yaro”. A yau […]
Barkanmu da warhaka uwargida. Ko kun san cewa miyar kuka hadaddiyar miya ce kuwa? Mutanen karkara da dama sun tsane ta ko kun san dalilinsu? Babu wani dalili illa ba su san yadda za su sarrafata ba ce. Kuka miya ce ta babban gida, inji masu magana suka ce “Kuka hana kukan yaro”. A yau na kawo muku miyar kukar da in aka bi wannan salon girki aka girka ta dole ne ta yi dadi. A sharba lafiya.
Abubuwan da za a bukata
- Kuka
- Attarugu
- Daddawa
- Albasa
- Bandar kifi
- Nama
- Magi
- Man ja
Hadi
Da farko za a dora ruwa a wanke nama sai a yayyanka masa albasa da gishiri kadan. Sannan a rufe ya yi ta dahuwa har sai naman ya yi laushe yadda tsohuwa marar hakora za ta iya ci. Sai a sauke a ajiye a gefe.
A kara ruwa kadan a kan silalen romon naman sannan a yayyanka albasa sai a daka daddawa a zuba da jajjagen attarugu mai tafarnuwa. A wanke bandar kifi a zuba. Su yi ta tafasa har sai bandar ta nuna sannan a zuba magi da manja a rufe su kara tafasa.
Bayan haka sai a zuba kuka kadan a rika kadawa ko da maburgi ko cokali domin kada a samu gudaji a ciki. Sai a dan rufe bayan ya dan tafasa sai a sauke.
Za a iya cin wannan miya da tuwon samobita ko masara ko na shinkafa.