Yadda ake miyar wake
Barkanmu da warhaka uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya kamar kullum. A yau na kawo muku yadda ake miyar wake. An fi sanin Nufawa da yin irin wannan miya ta wake, domin tana cikin abincinsu na gargajiya. Suna kiran miyar da suna ‘Ezowa’ wato miyar wake. Yana da kyau uwargida ta koyi girke-girke […]
Barkanmu da warhaka uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya kamar kullum. A yau na kawo muku yadda ake miyar wake. An fi sanin Nufawa da yin irin wannan miya ta wake, domin tana cikin abincinsu na gargajiya. Suna kiran miyar da suna ‘Ezowa’ wato miyar wake. Yana da kyau uwargida ta koyi girke-girke na kabilu daban-daban domin hana maigida cin abinci a waje, da kuma sanya kunnensa motsi. An fi hada irin wannan miya da tuwon shinkafa.
Abubuwan da za a bukata
• Wake
• Man ja
• Attarugu
• Gasasshen kifi (banda)
• Albasa
• Gishiri da magi
Hadi
Idan uwargida ta samo wakenta, sai ta jika shi. Bayan haka, sai ta cire kowar jikin waken. Sai ta dora ruwa a wuta. Bayan ya tafasa, sai ta zuba waken ya yi ta tafasa, har sai ya nuna ya yi lukwi. Sannan sai ta zuba yankakkiyar albasa da dakakken attarugu da manja da kifi banda (wankakke). Sai a jira miyar ta yi ta tafasa na tsawon mintuna kadan, sannan sai a zuba magi da gishiri. Hhmmn! Lagwada! Ana iya cin wannan miya da tuwon shinkafa. Kuma an fi son dafa wannan girkin da rana ko da yamma. Lallai idan maigida ya ci wannan abincin sai kunnensa ya motsa. Da fatan za a girka wa maigida wannan miyar domin armashi da kuma dandano mai gamsarwa!