Yadda ake ‘plantain pie’
Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Lallai akwai nau’ukan abinci daban-daban wanda kabilu da dama ke yi. Yana da kyau mace watarana ta shiga dakin girkinta domin gwada sabon abu. Abu wadda ba a ko ina aka taba yin sa ba wadda kuma zai yi dadi. A yau dai […]
Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Lallai akwai nau’ukan abinci daban-daban wanda kabilu da dama ke yi. Yana da kyau mace watarana ta shiga dakin girkinta domin gwada sabon abu. Abu wadda ba a ko ina aka taba yin sa ba wadda kuma zai yi dadi. A yau dai na kawo muku yadda ake ‘plantain pie’.
Abubuwan da za a bukata
• Ayaba
• kwai
• Magi
• Tafarnuwa
• Citta
• Kori
• Attarugu
• Koren tattasai
• Albasa
• Takardar foil
Hadi
A yayyanka albasa da danyen tafarnuwa da citta kanana, sannan a daura man gyada a wuta. Idan ya yi zafi sai a zuba albasa da yankakkiyar tafarnuwa da citta a gaurayasu. Sannan a zuba yankakken tattasai da da yankakken karas ayi ta soya su, sai a zuba magi da kori sannan a dauko kwai kamar hudu ko biyar a fasa a ciki ayi ta gaurayawa har sai ya soyu sannan a kwashe a ajiye a gefe.
A bare ayaba sannan a silala shi kamar yadda ake yin danbun tsaki. Bayan ya nuna sai a saka a kwano a daddana ta da ludayi. Sai a wanke hannu a goge sannan a shafa mangyada a tafin hannu sannan a mulmula ayabar a shimfideta a kan takardan ‘foil’ sai a baza ta kamar yadda ake ‘meat pie’ sannan a zuba wannan kwan a cikinta sai a rufeta da dayan gefen. A sami cokali mai yatsu a daddana bakin. Sai a daura man gyada a wuta bayan ya yi zafi sai a rika jefawa idan ya soyu sai a ajjiye a gefe.
Za a iya cin wannan girkin da shayi a matsayin abin karyawa da safe.