Yadda ake rubutun sha ɗan kamfani a Turai

Wani sabon salon rubutun sha na zamani da ya ɓullo daga kasashen waje ya tayar da kura, inda jama’a da dama, ciki har da alarammomi ke ce-ce-ku-ce a kansa.

Yadda ake rubutun sha ɗan kamfani a Turai

Wani sabon salon rubutun sha na zamani da ya ɓullo daga kasashen waje ya tayar da kura, inda jama’a da dama, ciki har da alarammomi ke ce-ce-ku-ce a kansa.

A yayin da wasu ke ganin cewa cigaban zamani ne ya shigo harkar neman tsari a addinance, masu ra’ayin sukan shan rubutun na ganin rashin dacewar hakan.

Akwai kuma masu ganin neman kudi ta kowace hanya ce ta sa ta kasar China — wadda a wasu sassan kasar ake hana Musulmi yin ibada — ta shiga wannan harkar, wanda kuma ke iya zama wasa da addini.

A gefe guda kuma, alarammomi da almajiransu da ke yi wa masu bukata rubutu domin wankewa su sha, na ganin wannan fasahar a matsayin barazana ga harkarsu.

Yadda abin yake

Shi dai wannan rubutun sha ɗan kamfani an sarrafa shi ne da salon daga-buhu-sai-tukunya, inda aka rubuta ayoyin da addu’o’insa da bugun inji a jikin takardu na musamman masu sauƙin sarrafawa (kamar toilet paper).

Sannan ba sai mai bukata ya wanke rubutun da ruwa yadda aka saba yi ba, kafin a sha.

Ayoyin da addu’o’in an buga su ne a jikin kananan takardu da ba su fi fadin tafin hannu ba, ko sukan ɗan dara fadin hannu; sai dai kawai mai bukata ya saya ya tsoma a ruwa daidai bukatarsa.

Daga ciki, akwai fakitin da ke dauke da Alkur’ani Izu 60 a jikin takardu kwara 8 kacal, akwai kuma kwalin ayoyin lalata sihiri, da ayoyin kariya, da wasu addu’o’i na musamman, kowanne da kudinsa.

Idan aka tsoma takardar a cikin ruwan, tawadar jikinta zai narke a ruwan cikin dan kankanin lokaci, sai mutum ya kwankwaɗe abinsa.

Ruwan tawadar kuma an yi ne daga sinadaran da za a iya ci ko a sha, marasa illa ga lafiyar dan Adam.

Aminiya ta ga bidiyon yadda wasu ke jika takardun a ruwa su sha, wasu kuma a cikin shayi, ko a madara.

A cikin jerin kayan da ke cikin setin akwai wasu kayan hadi kamar ganyen magarya da sauransu.

Alarammomi sun damu

Ganin bidiyon wannan rubutun sha dan kamfani daga kasar waje ya sa wasu alarammomi a soshiyal midiya bayyana fargabarsu cewa zai kashe musu kasuwarsu.

Bisa abin da aka saba, masu buƙatar rubutun sha sukan sa alarammomi ko almajirai su yi musu ne, musmman saboda guje wa kuskuren rubutu, wahalar rubutun allo, ko yawan abin da za a rubuta.

Idan alarammomi ko almajiran sun kammala kuma sai a ba su abin hasafi.

Wasu daga cikin waɗanda suka yi tsokaci kan lamarin na zargin kamfanonin kasar China da neman kashe wa alarammomi kasuwa da wannan fasaha.

Shin kasuwar alarammomi za ta mutu?

Amma Aminiya ta gano cewa kamfanin da ya kirkiro fasahar ba a kasar China yake ba, hasali ma ba a nahiyar Asiya yake ba.

Kamfanin mai suna Quranfi, a nahiyar Turai yake kuma a kasar Netherlands.

Bugu da kari, da alama alarammomi da ke nuna fargabarsu za su kwantar da hankalinsu, domin kuwa da wuya mutane masu matsakaici ko karamin karfi su  iya saya, saboda da tsadarsa.

Aminiya ta ziyarci shafin Quranfi, inda ake sayar da rubutun ta intanet ga duk masu bukata a fadin duniya, inda muka ga ana sayar da fakitin rubutun mafi sauƙin ne a kan Naira dubu talatin da 800, a yayin da mafi tsada kuma farashinsa ya kai Naira 307,400.

Daga ciki, ana sayar da fakitin takardun rubutun Suratul Baƙara a kan N30,800 kowane fakiti, haka ma na Suratu Maryam da na Suratus Saffat da ayoyin lalata sihiri.

Babban setin ayoyin kariya kuma N307,400 wanda a ciki har da wasu kayan hadi, matsakaicinsa kuma N215,200.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta