Yadda ake sabon girkin kamoniya
Uwargida barkanmu da warhaka. Na san za a ce na taba girka kamoniya. Haka ne amma kuma wannan dahuwar daban take da wancan wadda ake sanya lemun tsami a ciki. Ya kamata a koyi yadda ake dahuwar abinci daya salo daban-daban. Misali, idan shinkafa za a dafa, akwai mai miya da dafa-duka da kuma soyayyiyar […]
Uwargida barkanmu da warhaka. Na san za a ce na taba girka kamoniya. Haka ne amma kuma wannan dahuwar daban take da wancan wadda ake sanya lemun tsami a ciki. Ya kamata a koyi yadda ake dahuwar abinci daya salo daban-daban. Misali, idan shinkafa za a dafa, akwai mai miya da dafa-duka da kuma soyayyiyar shinkafa. Yana da kyau a koyi salon dafa girki daban-daban domin kada ya ginshi maigida.
Abubuwan da za a bukata
• Kayan ciki (ban da hanji)
• Albasa
• Attarugu da tattasai
• Man gyada
• Magi
• Kori
• Da ganyen ‘thyme’.
• Tafarnuwa
Hadi
Idan uwargida ta wanke kayan ciki ya fita fes, walau na rago ko na saniya ko akuya, ta wanke yadda karnin zai fita, sai ta dauko albasa ta yanka. Ta dauko tattasanta da attarugunta ta jajjaga su a turmi tare da tafarnuwa. Idan ta gama, sai ta samo roba ta zuba kayan cikin a ciki da jajjagen attarugu da tattasai da tafarnuwa da albasa da kori da magi da ganyen ‘thyme’. Sai ta yaryada magi a kai da kori sai ta gauraya su sannan sai ta sa a firiji na tsawon minti 5 kafin ta ciro. Sannan sai ta dauko tukunya ta juye wannan hadin a ciki. Ta zuba man gyada kadan sannan ta dora a kan wuta. Ruwan jikin kayan cikin zai fito. Daga nan sai ta rika gauraya hadin a kan wuta har sai ya nuna sannan ta kwashe. Ana iya hadin wannan kamoniyar ce da soyayyiyar doya wadda aka dafa kuma aka sake soya ta. Za a iya yin wannan hadin wa maigida kafin ya fita aiki da kuma yara.