Yadda ake sakaci da magungunan cututtukan dabbobi duk da hadarinsu

Yamutsin da aka samu kan magungunan yaki da kwayoyin cututtukan  dabbobi yana haifar da tabarbarewar kiwon lafiya a duniya. Annobar ta fi yawa a Afirka ta Yamma musamman Najeriya a fannin kiwon Kaji. Magungunan yaki da kwayoyin cutar ana amfani da su ne saboda dalilai uku: wato a samar da saurin girman dabbobi da tsuntsaye, […]

Yadda ake sakaci da magungunan cututtukan dabbobi duk da hadarinsu

Yamutsin da aka samu kan magungunan yaki da kwayoyin cututtukan  dabbobi yana haifar da tabarbarewar kiwon lafiya a duniya. Annobar ta fi yawa a Afirka ta Yamma musamman Najeriya a fannin kiwon Kaji.

Magungunan yaki da kwayoyin cutar ana amfani da su ne saboda dalilai uku: wato a samar da saurin girman dabbobi da tsuntsaye, a kare alamomin murar tsuntsaye a jikinsu da ke sanya cuta a jiki da kuma yin rigakafin wata cuta da ke iya kawo masu farmaki nan take.

Magungunan yaki da kwayoyin cutar dabbobin suna da sinadarai masu karfi da suke yakar kwayar cutar bakteriya, amma in cutar ta habaka wadannan magunguna ba su iya yi mata komai sai an samu na gaba da su wajen karfi wato Antimicrobial Resistance(ARM) saboda cutar ta haifar da kananan kwayoyin cutar bakteriya da bairus da cima-kwance, sinadarin ARM yana kashe su ba tare da bata lokaci ba.

Dakta E. Wesangula AMR jami’i ne a Ma’aikatar Lafiya ta Kenya, a babban taron Afirka da aka kammala kwanan nan a Nairobi babban birnin Kenya kan ‘Kimiyyar Manema Labarai’ ya fitar da bayani kan hadarin da ya tinkaro kiwon lafiyar mutane sakamakon watsuwar magungunan yaki da kwayoyin cutar dabbobi.

Matsayarsa ta dace da abin da Kungiyar Likitocin Dabbobi ta Najeriya da Farfesa Mohammad Bello Agaie ke shugabanta ta nuna na damuwa da lamarin.

Dokta Wesangula ya ce a yanzu mutane sun fi mayar da hankali ga magungunan yaki da kwayoyin cututtukan dabbobi fiye da na lafiyarsu, kuma masana kiwon lafiya suna nuna damuwarsu kan wannan. “A kauyuka masu yawa manoma na amfani da magungunan yaki da cututtukan mutane ga kaji domin su warkar da su daga wasu cututtuka da suka same su,” inji shi. Sai ka ga kaza ba ta da lafiya an jika mata kwayar farasitamol, ko kafino da sauransu.

Cin nama da kwai ko madara da suke dauke da magungunan kwayoyin cuta, suna haifar wa mutum sinadaren cutar da ba a gani wadanda kwayoyin magani ba su kashewa sai a yi ta fama a lokacin da ka kwanta rashin lafiya.

Farfesa Bello Agaie, ya bayyana yadda magungunan kwayoyin cututtukan dabbobi  da ake amfani da su suke zama hadari ga mutane “A duk lokacin da aka sanya wa dabbbobi a abincinsu suka ci to a kyale dabbobin har zuwa wani lokaci kada a yanka su, idan ba a yi haka ba za a samu ragowar kwayoyin a cikin madara ko namansu. Ka ga in ka ci nama, kwai ko ka sha madara ina fada maka ka ci wadannan magungunan kwayoyin cutar a fakaice,” inji shi.

Farfesa Agaie ya ce, abin da yake a zahiri “Abin ya fi muni a kiwon kajin gona. Ba ruwan mutane da kiyaye ka’idojin magani suna iya hada kwaya biyu ko uku ko hudu wuri daya a ruwa ba ruwansu da tsuntsayen suna da ciwo ko lafiyarsu kalau, damuwarsu dai girmansu ko su girma da cuta su dai ba su damu ba,” inji shi.

“Abin da ke faruwa ke nan a tsakanin kaji masu yin kwai da masu girman nama, mutane na cin kwayoyin cuta a fakaice da sun tafi asibiti don wata rashin lafiya a yi ta ba su magani ba su samun sauki don suna dauke da kwayoyin cutar da ke kashe maganin da ake ba su, saboda kananan kwayoyin cutar sun san yadda suke guje wa  maganin da ake ba su ba zai shafe su ba. In kuma ka ce, ba ka cin nama ko kwai ko shan madara sai dai ka rika cin kai da kafafu da bindin saniya kana kara wa kasa taki domin shuka, wannan ma magani ne mai kwayoyin cuta a cikinsa.” inji shi.

Ciyawar da ake samar wa dabbobi tana dauke da ragaggun magungunan kwayoyin cutar kuma tana rage kaifin magani, abin da ke sanya kwayoyin cutar habaka in an bayar da maganin kwayoyin cutar su kasa kawar da ita.

A cewar Dokta Wesangula kusan mutum miliyan 4.2 a Afirka ne ake sa ran su rasa rayukansu matukar ba a samu maganin da zai kawar da kwayoyin cututtukan dabbobin ba.

A kididdigar Bankin Duniya kan sha’anin lafiya za a kashe Dalar Amurka tiriliyan 32 zuwa shekarar 2050 kan wannan lamari.

Daga yanzu zuwa shekarar 2050 ya ce, kiwon dabbobi da yake kasa da mataki na kashi 2.6 cikin 100 zai haura zuwa kashi 7.5 cikin 100 a kowace shekara.

A yanzu duniya ta hau turba ta yakar matsanancin talauci (a duk yini mutum ya rika mallakar Dala Amurka 1.90) zuwa shekarar 2030 da kudirin fitar da kashi uku na mutanen duniya cikin talauci da samar da magungunan kwayoyin cutar dabbobi, kamar yadda rahoton Bankin Duniya na shekarar 2016 ya fitar.