Yadda ake salad din dankali
Assalamu alaikum Uwargida tare da fatar alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Akwai hanyoyi da dama da mata ke yin salad; walau na latas ko kabeji da makamatansu. Kamar yadda nake bayani a kan canja nau’o’i da salon girke-girke ne saboda kada ya ginshi masu ci. Hakan ya sanya a yau na kawo muku yadda […]
Assalamu alaikum Uwargida tare da fatar alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Akwai hanyoyi da dama da mata ke yin salad; walau na latas ko kabeji da makamatansu. Kamar yadda nake bayani a kan canja nau’o’i da salon girke-girke ne saboda kada ya ginshi masu ci. Hakan ya sanya a yau na kawo muku yadda ake hadin salad din dankali. Tare da fatar za a gwada irin wannan hadi a gida. A sha karatu lafiya.
Abubuwan da za a bukata
- Dafaffen dankalin Turawa
- Karas
- Kwai
- Sausage ( za a iya samu a manyan shagunan sayar da kayan abincin zamani)
- Bama
- Sukari
- Ruwan lemun tsami
- Naman kaza
Hadi
A fere dankalin Turawa sannan a tafasa a wuta da dan gishiri kadan. A yayyanka karas kanana a wanke sannan a tafasa shi kamar tafasa daya sannan a sauke. A samu cinyar kaza a sulala ta da kayan kanshi da dandano har sai ruwan ya shanye sannan a soya ta a ajiye a gefe. A tafasa Sausage da ruwan gishiri kadan sannan a soya sama-sama yadda ba zai dade a kan wuta ba sannan a sauke. A yayyanka shi kanana.
A samu kwano a zuba yankakken dankalin Turawa da karas da Sausage da soyayyen naman kazar.
Bayan haka a kwaba Bama a wani karamin kwano da ruwan lemun tsami da sukari sannan a dora a kan hadin dankalin da su karas din. Za a iya cin wannan salad da dafaffiyyar shinkafa ko a kan dafa-dukar shinkafa. A ci dadi lafiya!