Yadda ake soyayyar taliya da kaza

Assalamu alaikum Uwargida yaya sanyi? Allah Ya fitar da mu lafiya. A yau na kawo muku yadda ake soyayyar taliya da kaza. Kowace mace tana da irin nata dabarun wajen sarrafa girki. Yana da kyau mata su rika canza yanayin yadda suke sarrafa girki domin shi harshe a kullum yana son dandano  daban-daban. Yana da […]

Yadda ake soyayyar taliya da kaza

Assalamu alaikum Uwargida yaya sanyi? Allah Ya fitar da mu lafiya. A yau na kawo muku yadda ake soyayyar taliya da kaza. Kowace mace tana da irin nata dabarun wajen sarrafa girki. Yana da kyau mata su rika canza yanayin yadda suke sarrafa girki domin shi harshe a kullum yana son dandano  daban-daban. Yana da kyau mace a kullum ta kasance kwararriya a wajen sarrafa girki.

Abubuwan da ake bukata:

• Taliya

• Tumatir

• Nama

• Kaza

• Karas

• Koren wake

• ‘peas’

• Magi

• Kori

• Tafarnuwa

• Citta

• Albasa

Hadi:

A dora ruwa a wuta, bayan ya tafasa sannan a zuba taliya da gishiri kadan. Idan ta yi tafasa daya sai a tsame. A dora man gyada a wuta sannan a zuba yankakkiyar albasa da yankakken tumatir da jajjagaggen attarugu. A tafasa nama sannan a yayyanka shi kanana sannan a zuba. A zuba magi, kori da garin tafarnuwa da citta sannan a dauko wannan taliyar a zuba ta a ciki a gauraya. A zuba ruwa kadan sannan a   rufe bayan mintuna biyar a sauke.

A tafasa kaza ta yi laushi hade da magi da kayan kanshi sannan a soya da man gyada. A soya tumatir da attarugu da albasa. A zuba magi da citta da tafarnuwa. Bayan sun soyu sannan a dauko kazan a cakuda shi a ciki sannan a dora a kan wannan soyayyar taliyar.