Yadda ake tazarar haihuwa (2)
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ire-iren hanyoyin aiwatar da tazarar haihuwa na wucin gadi, alfanu da hadurran da ke tattare da su. Da fatan Allah Ya sa bayanin ya isa ga masu bukatarsa, musamman wadanda suka aiko da tambayoyi, amin. 1. Murfin […]
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ire-iren hanyoyin aiwatar da tazarar haihuwa na wucin gadi, alfanu da hadurran da ke tattare da su. Da fatan Allah Ya sa bayanin ya isa ga masu bukatarsa, musamman wadanda suka aiko da tambayoyi, amin.
1. Murfin Mahaifa: Ana tura shi cikin ‘yanmatancin mace kafin gabatarwar ibadar aure, don rufe kofar mahaifa wajen haduwar kwan haihuwar mace da maniyyin namiji. Murfin mahaifa iri hudu ne, Diaphragm da cerbical cap da contraceptibe sponges da kuma cerbical shields.
I. Diaphragm wata ‘yar roba ce kewayayyiya mai kamar masa ko waina, ana tura shi cikin ’yanmatancin mace ya rufe kofar mahaifa, don hana maniyyin namiji shiga ciki.
Yadda Ake Amfani da shi: Da farkon sawa, dole sai jami’an lafiya za su auna don sanya wa mace wanda ya yi daidai da kofar mahaifarta, kasancewar kowace mace fadi da yanayin kofar mahaifarta daban da ta wata. Kuma su Jami’an lafiya ne za su karantar da mace yadda za ta rika amfani da shi. Ana shafe shi da maganin da ke kashe maniyyi, kuma ana so a tura shi awa biyu kafin gabatarwar ibadar aure, sannan a bar shi sai bayan awa shida da gabatarwar kafin a cire. In kuma da yiwuwar sake yin ibadar aure, dole sai an sake sa wani magani kashe maniyyi. Ba a son a bar shi a jiki ya wuce kwana daya, domin hakan na iya haifar da yaduwar kwayoyin cuta a cikin ‘yanmatanci har su samu damar shiga jini su haifar da matsananciyar cuta manyan namomin jiki irin su hanta, (todic shock syndrome).
Idan an sa kulawa sosai wajen amfani da shi, wannan kalar murfin ’yanmatanci yakan yi shekara biyu ana amfani da shi bai lalace ba.
Matsalolinsa:
Dole sai jami’an lafiya sun auna kafin fara amfani da shi.
Dole sai an sake tura wani maganin kashe maniyyi cikin ’yanmatanci idan za a sake gabatar da ibadar aure.
Gubar ’yanmatanci da ake shafawa na iya haifar da kuraje ko salewar ’yanmatanci.
Yana sa ciwon mafitsara ga wasu matan.
Yana kawo yaduwar kwayoyin cuta in ya dade cikin jiki.
II. Cerbical Cap: Murfin mahaifa ne na roba mai siffar murfin bulunboti, wanda ake amfani da shi wajen rufe ’yanmatanci mace lokacin saduwa, don hana shiga ciki. Shi wannan murfin yakan datse kofar mahaifa sosai fiye da diaphram. Kuma yana aiki har na tsawon kwana biyu bayan ibadar aure.
Yadda Ake Amfani Da Shi: Ana tura shi cikin ’yanmatanci bayan an shafe shi da maganin da kashe maniyyi, sannan a tabbatar ya shiga kofar mahaifa sosai.
Matsalolinsa:
Yana sa fitowar kuraje a ’yanmatanci ko salewar fata, musamman in aka bar shi ya dade sosai.
Yana sa yaduwar kwayoyin cuta in aka bar shi ya dade sosai.
III. Contraceptibe Sponges: Wani soso ne mai dauke da gubar da ke kashe maniyyi, wanda ake tura shi cikin ’yanmatanci don rufe kofar mahaifa da kashe maniyyin namiji. A hankali gubar da ke jikin soson ke digewa tana shiga cikin ’yanmatanci tana kashe maniyyi.
Yadda Ake amfani da shi: Da farko za a jika shi da ruwa kimanin karamin cokali biyu, a tabbata ruwan mai tsabta ne, sannan a dan murza don ruwan ya game ko ina, wannan shi zai jikar da gubar da ke kasha maniyyin da ke ciki; sannan a hankali a rika tura shi cikin ’yanmatanci kuma a tabbatar ya shiga ciki sosai ya rufe kofar mahaifa.
Ib. Cerbical Shields: Shi ma wani murfin mahaifa ne na zamani, sai dai shi jijiyoyin ’yanmatanci ne ke rike da shi ba ya mannewa a kofar mahaifa kamar sauran.
Yadda ake amfani da shi: Ana shafe shi da gubar da ke kashe maniyyi, sannan a tura shi can cikin ’yanmatanci, da ya shiga ciki, shi da kansa zai daidaita kuma ya rufe kofar mahaifa sosai.
Matsalolinsa:
Yana da wuyar sawa.
Yakan sa ciwon mafitsara ga wasu matan.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.