Yadda ake tazarar haihuwa (3)
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ire-iren hanyoyin aiwatar da tazarar haihuwa na wucin-gadi, alfanu da hadurran da ke tattare da su. 2. Dakatar da haihuwa ta hanyar sarrafa Sinadaran Jinsi (Sed Hormones): Ana sarrafa sinadaran jinsin ’ya mace, watau progesterone da estrogen; […]
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ire-iren hanyoyin aiwatar da tazarar haihuwa na wucin-gadi, alfanu da hadurran da ke tattare da su.
2. Dakatar da haihuwa ta hanyar sarrafa Sinadaran Jinsi (Sed Hormones): Ana sarrafa sinadaran jinsin ’ya mace, watau progesterone da estrogen; ta hanyoyi da dama don hana yiwuwar shigar ciki na wani lokaci. Lokacin da wadannan sinadarai suka shiga cikin jini, suna hargitsa asalin tsarin da yabanyar ’ya mace yake a kai, ta hanyar:
• Hana kyankyasar kwan ’ya mace daga jakar kwayayenta zuwa mahaifa, (obulation).
• Suna kara kaurin yaukin da ke cikin zauren mahaifa, don hana kwayayen haihuwar da namiji motsawa, ballantana har su isa ga inda kwan haihuwar ’ya mace yake.
• Suna canza yanayin hanyar da kwan haihuwar mace ke bi daga ma’ajiyarsa zuwa mahaifa.
Hanyar sarrafa sinadaran jinsi wajen hana daukar ciki tana da inganci sosai, kuma ma’aurata da yawa sun fi zabarta sama da sauran, musamman da yake ba ta tattare da matsalar rage karsashin sha’awa, kuma ba a bukatar sawa da cirewa irin na sauran hanyoyin da bayaninsu ya gabata.
2. Hanyoyin Sarrafa Sinadaran jinsi don dakatar da haihuwa:
1. kwayoyin Hana Shigar Ciki (Pills): kwayoyi na hadiya da ake sha, don dakatar da haihuwa har zuwa wani lokaci. Wadannan kwayoyi iri biyu ne: akwai wanda ake hada sinadarin estrogen da progestin a cikin kwaya daya, akwai kuma wanda progestin din ne kadai a ciki. Ana shan kwaya daya kullum na tsawon kwana ashirin da daya, sannan a dakata kwana bakwai ba a sha ba, sannan kuma a sake ci gaba da sha kullum na tsawon wasu kwana ashirin da daya, sannan a sake dakatawa, haka za a yi ta yi har zuwa tsawon lokacin da ake son a dakatar da haihuwar. In an dage ba a tsallake wajen shan kwayoyin ba, akwai tabbacin cewa da wuya a samu shigar ciki ta hanyar.
2. Allurar Hana Shigar Ciki: Ita ma kamar kwayoyin suke, iri biyu ce: akwai mai progestin zalla wacce ake yi duk bayan wata uku, watau tana hana daukar ciki har na tsawon wata uku; dayar kuwa mai hade da sinadaran biyu wata estrogen da Progestin ana yinta duk bayan wata daya, watau tana hana shigar ciki na tsawon wata daya ne kadai.
3. Dashen Hana Shigar Ciki (Hormonal Implants): Wannan wani dan karamin bututun roba ne, dai-dai da girman tsinken ashana, wanda ke cike da sinadarin progestin; ana tsaga cinyar hannun mace, sannan a dasa shi ciki, a hankali zai rika shigar da sinadarin cikin magudanar jini. Yana hana haihuwa na tsawon shekara uku zuwa biyar. Yakan haifar da kecewar jinin haila ga wasu matan, yayin da wasu kan sa su kara nauyin jiki; wasu kuma ya ramar da su. Akwai yiwuwar yaduwar kwayoyin cuta daidai inda aka tsaga aka sanya wannan tsinke, ko kuma fatar wajen da aka tsaga din ta canza launi.
4. Facin Hana Shigar Ciki (contraceptibe patch): Wannan wata roba ce mai kamar soson shafa hoda a ganin ido, wacce ke dauke da sinadaran jinsin ’ya mace, watau estrogen da progestin. Ana lika ta duwawu da baya da cinyar hannu, ko saman ciki sau daya a sati har na tsawon sati uku, sannan a dakata na sati daya sannan a ci gaba. Fatar jiki za ta rika tsotsar sinadaran suna shiga cikin magudanar jini a hankali, su yi aikin hana shigar ciki kamar yadda ya gabata a bayani.
5. Zoben ’Yanmatanci (contraceptibe ring): Wani zobe ne da ke dauke da sinadaran jinsin ’ya mace estrogen da progestin, ana tura shi can cikin ’yanmatanci a bar shi a ciki na tsawon sati uku, sannan a yi hutun sati daya, sannan a sake sa wani sabon zoben shi ma a bar shi a ciki na tsawon sati uku. Bambancinsa da murfin mahaifa shi ne, ba ya bukatar sai jami’an lafiya sun sanya shi, kuma ba ya bukatar hada shi tare da gubar diyan maniyyi. Zai iya kaikayin gaba da yawan zubar ruwa daga ’yanmatanci ga wasu matan.
6. kwayoyin Taimakon Gaggawa (Emergency Pills): Wadansu kwayoyi ne da aka tanada musamman don bayar da taimakon gaggawa, duk lokacin da ma’auratan da ba su son haihuwa suka yi ibadar aure ba tare da yin amfani da daya daga cikin hanyoyin hana shigar ciki ba, sai mace ta sha wannan kwayoyi take yanke shan su na hana haduwar kwayayen haihuwar mace da namiji. Ana shan su sau biyu bayan awanni sha biyu tsakani. Kamar kwayoyin dakatar da haihuwa suke, sai dai su an zuzuta yawan sinadaran da ke cikinsu sama da kwayoyin hana shigar ciki da ba na taimakon gaggawa ba.
7. kananan kwayoyin Hana Shigar Ciki (Mini Pills): An tanade su ne musamman don mata masu shayarwa, suna dauke da sinadarin progestin kadai, shi ma din a karamin awo.
Matsalolinsa Amfani da Sinadaran Jinsi Wajen Hana Shigar Ciki:
Matsalolin da wannan hanyar dakatar da haihuwa ke haifarwa ya danganta daga wannan macen zuwa wata, akan dace wasu bai haifar masu da kowace irin matsala ba, wasu zai dan takura musu kadan ta yadda har takurar ma ba za ta dame su ba, yayin da wasu zai haifar musu da matsaloli da yawa, ta yadda har ba su marmarin sake yin amfani da shi. Haka kuma wata hanyar na iya haifar da matsala ga mace, amma in ta canza zuwa wata kuma sai a ga an dace da rashin matsala a cikinta. Don haka yana da matukar alfanu kafin fara amfani da wata hanyar dakatar da haihuwa, ma’aurata su tabbatar sun yi bincike mai kyawu, kuma sun tace sun tantance don kada garin neman kiba a samo rama. Ga jerin matsalolin da wannan hanya ta sarrafa sinadaran jinsi ke haifarwa ga wasu matan:
• Akan sami jinkirin wata biyu zuwa uku kafin tsarin daukar ciki na asali ya koma daidai, duk lokacin da ma’aurata suka bukaci ci gaba da samun haihuwa. In aka samu rashin dacewa, wasu matan ma har sukan yi watanni ko shekaru haihuwarsu ba ta dawo ba, har ta kai ana neman taimakon don neman samun dawowarta.
• Yana sa rikirkicewar shau’uka; tsananin huzni, ciwon kai, hawan jini da kurajen fuska.
• Yana sa kumburewar wajen shayarwa kuma da yawan digar ruwan nono daga waje.
• Akwai yiwuwar kara hadarin kamuwa da cutar sankara (cancer) na mahaifa, zauren mahaifa, da kuma na wajen shayarwa.
• Yana sa rikirkicewar jinin haila ga wasu matan; wasu ya dauke musu gaba daya, wasu sai bayan wata 2 zuwa uku, wasu ya rika zuba da yawa, wasu kuma ya rika zuba kadan-kadan sannan a-kai-a-kai.
• Yana sa karuwar nauyin jiki da ciwon mara ko kugu ga wasu matan
• Yana kusanto da kamuwa da cutar ciwon siga, ciwon zuciya da hawan jini ga wadanda akwai yiwuwar cutar ta bayyanar gare su can gaba a rayuwa.