Yadda ake tazarar haihuwa (4)

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ire-iren hanyoyin aiwatar da tazarar haihuwa na wucin gadi da alfanu da hadurran da ke tattare da su. Da fatan Allah Ya sa bayanin ya amfanar da masu bukatarsa, musamman wadanda suka aiko da tambayoyin. 3. Lura […]

Yadda ake tazarar haihuwa (4)
Yadda ake tazarar haihuwa (4)

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ire-iren hanyoyin aiwatar da tazarar haihuwa na wucin gadi da alfanu da hadurran da ke tattare da su. Da fatan Allah Ya sa bayanin ya amfanar da masu bukatarsa, musamman wadanda suka aiko da tambayoyin.

3. Lura Da Yanayin Jiki Don Hana Shigar Ciki:
Wannan ya kunshi tsananta lura da sa ido ga canzawar yanayin jiki da ke bayyana lokacin gabatowar jinin haila, haka mace za ta rika lura har ta gano ranakun yabanyarta, wadanda idan mijinta ya kusance a wadannan ranakun, lallai za ta samu shigar ciki. Idan aka tabbatar da wadannan ranaku, sai ma’aurata su rika tsallake wadannan ranakun wajen ibadar aure, ko kuma su yi mafani da wata hanyar hana shigar ciki a wadannan ranaku na cikar yabanya.
Yadda ake kyankyasar kwan Haihuwar Mace
Kamar yadda aka san mace da yin jinin haila ko wane wata, kyankyasar kwan haihuwarta ne ke kaiwa ga zubar jinin haila. Kowane wata kwai daya ke nuna daga jakar kwayayen haihuwar ’ya mace, idan kwan haihuwar ya gama nuna sai a kyankyashe shi, ya bi hanya zuwa mahaifa. Da zarar an kyankyashe kwan haihuwar mace, to lokacin cikar yabanyarta ya fara ke nan.
kwan haihuwar mace yakan dauki kwana uku zuwa biyar kafin ya isa mahaifa. A lokacin da kwan ke tafiya, shimfidar mahaifa za ta cika, ta kara kauri, don bayar da dama ga kwan haihuwar namiji saukin isa ga kwan haihuwar ’ya mace. In ibadar aure ta faru a wannan lokaci, in Allah Ya so kuma aka samu shigar ciki, shi ke nan sai cikin ya kafu a cikin mahaifa, ya ci gaba da girma. Idan kuma ba a samu shigar ciki ba, kwan zai ci gaba da zama na tsawon kwana uku zuwa biyar, kafin shimfidar mahaifar ta narke, sai a fitar da ita tare da kwan, wannan shi ne jinin haila. Idan mace ta tantance ranar da kwan haihuwarta ke kyankyasa, sai ta kiyaye wadannan ranaku, ta kididdige ranar maimaituwarsa a kowane wata, don kauce wa ibadar aure ko daukar wata hanyar hana shigar ciki a wadannan ranaku.
Hanyoyin da ake bi wajen kiyaye ranakun kyankyasar kwan haihuwa (Obulation):
1.    Kalandar Jinin Haila: Sai mace ta rika rubuta ranar bayyanar jinin hailarta, da haka har ta gano ranar da take kyankyasar kwan haihuwa, don guje wa yin ibadar aure a wadannan lokuta.
2.    Kiyaye Canzawar dumin Jiki: Mace kullum za ta dauki dumin jikinta da tsinken auna dumin jiki (thermometer), ana daukar dumin jikin ne kullum idan an tashi daga barci kafin a sauka daga wajen kwanciya. Duk ranar da ta ga dumin ya karu sama da na kullum, to ranar kwan haihuwarta na wannan wata zai kyankyashe.
3.    Canzawar ruwan maziyyi: Mace za ta sa ido ga yanayin ruwan maziyyinta. Maziyyin da ke fita lokacin kyankyasar kwan haihuwa fari ne, mai kauri, mai lema kuma mai laudi, yana taimakawa ga yiwuwar haduwar kwan haihuwar mace da namiji cikin mahaifa. Amma maziyyi kafin kyankyasar kwan haihuwa, da kuma gab da gabatowar jinin haila mai launin dorawa ne, sannan ba shi da kauri kuma ba shi da lema. Sai dai yawan shan kayan da’a da wasu matan ke yi na iya sa yawan  zubar ruwan maziyyi, don haka zai yi wuya su iya tantance ranakun kyankyasar kwan haihuwarsu ta wannan hanya.
4.    Tsinken IUD Don Hana Shigar Ciki: IUD wani siririn tsinke ne mai siffar harafin T, yana da siririn zare a kowane bangare, ana sanyak shi cikin mahaifar mace don hana shigar ciki, ko idan cikin ya shiga ya hana tsiruwarsa cikin mahaifa. IUD iri biyu ne, akwai wanda ke dauke da sinadarin copper, wanda a hankali zai rika turara cikin mahaifa, yana hana kwayayen haihuwar namiji isa ga kwan haihuwar mace ballantana har a samu ciki. Sannan akwai sabon samfurin wannan tsinken da ake kira da IUS, shi kuma yana dauke da sinadarin ’yanmatanci progestin, wanda shi ma a hankali sinadarin ke turara cikin mahaifa, ya hana shigar ciki ko kafuwarsa cikin mahaifa. Yana daukar tsawon shekara biyar zuwa goma yana aikin hana shigar ciki, ya  danganta da samfurin da aka yi amfani da shi.
Matsalolinsa:
•    Babbar matsalarsa ita ce, akwai yiwuwar a samu shigar ciki alhali yana cikin mahaifa, wanda hakan na iya sa wa cikin ya zube lokacin da ya kai wata hudu zuwa shida. Zubar da cikin da ya kai wata hudu kuwa haramun ne a shari’a.
•    Haka kuma akwai yiwuwar a samu tsiruwar ciki a wajen mahaifa, wanda hakan zai iya zama barazana ga lafiya da kuma rayuwar uwar da ke dauke da cikin, da kuma abin da za ta haifa.
•    Yakan sa yawan zubar jini tsakanin wannan haila zuwa wata, kuma yana sa jinin hailar ya kara yawa da nauyi.
•    Akwai yiwuwar tsinken IUD ya lume cikin mahaifa, kuma sinadarin copper da ke cikin IUD yana iya huda mahaifa.
•    Sannan yana sa yaduwar kwayoyin cuta a mara da ’yanmatanci da mahaifa.
5.    Shayarwa Don Hana Shigar Ciki:
Bayan haihuwa, uwa na iya yin amfani da shayar da nono ga danta wajen hana shigar ciki, matukar ta cika wadannan ka’idojin:
I.    Ya kasance ba a ciyar ko shayar da jaririn da komai sai nonon mahaifiyarsa kadai. Kuma za a rika shayar da shi kodayaushe, ba dare ba rana.
II.    Ya kasance a lokacin nan, jaririn bai kai wata shida da haihuwa ba.
III.    Sannan kuma ya kasance jinin hailar ita uwar bai dawo ba.
To in aka cika wadannan sharudda, suna hana shigar ciki har zuwa lokacin da aka fara ciyar da jaririn da wani abinci tare da nonon uwarsa
Sadaukarwa Don Hana Shigar Ciki: Haka kuma ma’aurata na iya sadaukar da yin ibadar aure gaba daya don hana shigar ciki har sai lokacin da suka so sake samun wata haihuwar. Ma’auratan da suka zabi yin tazarar haihuwa ta wannan hanya, ya kamata su zauna su tattauna tsakaninsu, su tabbar su sun amince da amfani da wannan hanyar don yin tazarar haihuwa, sannan su sanya iyakar lokacin da za su dauka suna sadaukarwar, su kuma sanya ka’idoji da suka dace da yanayinsu. Ma’aurata na iya kauce wa ainihin ibadar aure ta al’aura, amma za su yi cudanya da juna ta halartacciyar hanya, har su kai ga biyan bukatar sha’awarsu; yin hakan na da hadari, domin akwai yiwuwar a kasa daurewa, hakan kuma na iya kai wa ga shigar cikin da ba a shirya masa ba. Don haka sai ma’aurata su zabi abin da suka tabbatar za su iya, kuma zai fi musu sauki.