Yadda ake dafa Tuwon Shinkafa da miyar Ganyen Ugwu
A yau muna dauke ne da yadda za ki girka Tuwon shinkafa da miyar Ganyen Ugwu
Uwargida barka da rana.
A yau muna dauke ne da yadda za ki girka Tuwon shinkafa da miyar Ganyen Ugwu.
Kayan hadin da ake bukata
Tuwon shinkafa
Shinkafar tuwo
Ruwa
Yadda za a dafa tuwon
A jika shinkafar tuwo a ruwa ta jiku sosai, sai a dora ruwa a wuta, bayan ya tafasa sai a wanke jikakkiyar shinkafar a zuba sannan a rage wuta a rufe da murfin tukunya.
Sai a bar shi ya yi ta tafasa sai ya yi laushi sosai, sai a sauke a tuka
A kwashe a zuba a kwanuka.
Miyar ganyen Ugwu
Kayan hadi:
Ganyen Ugwun
Naman shanu ko na kaza
Ganda
Kifi
Albasa
Tumatir
Attarugu
Daddawa
Sinadarin dandano
Manja
Tafarnuwa
Yadda za a dafa miyar
- A wanke ganda da naman sannan a sanya a tukunyar.
- A yanka albasa a sa magi da gishiri sai a rufe a dora a kan wuta.
- Idan suka yi laushi sai a sauke a ajiye a gefe.
- A wanke ganyen ugwu da gishiri da ruwa sannan a yayyanka a ajiye a gefe.
- A wanke kifi sannan a yanka shi a ajiye a gefe.
- A dora tukunyar a wuta sannan a zuba manja.
- Idan manjan ya yi zafi, sai a zuba jajjagen kayan miya a yi ta soyawa har sai sun soyu.
- Sai a zuba magi da dadawa da dafaffen naman da ganda.
- Bayan ya dan tafasa sai a zuba ganyen ugwun a jira na tsawon minti sannan a sauke.