Yadda ake wasan ɓuya tsakanin ’yan gudun hijira da jami’an tsaro a Abuja
Iyalai da dama da ’yan fashin daji suka raba su da matsugunansu a wasu jihohin Arewa-maso-Yamma da Arewa-maso-Gabas sannan daga bisani kuma aka kore su daga birnin Abuja, inda suka samu mafaka a halin yanzu, suna wani hali a wasu sassan Jihar Nasarawa da ke makwaftaka da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Iyalai da dama da ’yan fashin daji suka raba su da matsugunansu a wasu jihohin Arewa-maso-Yamma da Arewa-maso-Gabas sannan daga bisani kuma aka kore su daga birnin Abuja, inda suka samu mafaka a halin yanzu, suna wani hali a wasu sassan Jihar Nasarawa da ke makwaftaka da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Binciken da wakilinmu ya yi ya nuna cewa, ’yan gudun hijirar sun fito ne daga sassan jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da Kebbi da Sakkwato a yankin Arewa-maso-Yamma da jihohin Adamawa da Borno da Yobe a yankin Arewa-maso-Gabas.
A yanzu haka galibinsu sun faɗa barace-barace da kananan ayyuka ko sana’o’in da ba su taka kara sun karya ba, domin samun abin kai wa bakin salati.
Wasu daga cikin mabaratan da muka zanta da su, sun bayyana cewa, sun fito ne daga yankunan karkarar da matsalar tsaro ta yi wa dabaibayi a yankunan biyu.
- Yadda Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass ya yi wa Tinubu addu’ar nasara
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 24 a Zamfara
A cewarsu, a baya sun kasance suna rayuwa cikin aminci da mutunci a yankunan nasu, inda suke kula da gonakinsu da dabbobinsu, sai dai bayan shafe shekaru ana tashe-tashe hankula na hare-haren ’yan fashin daji, lamarin da ya jefa su cikin baƙin talauci, inda mata da dama suka zama zawarawa, yayin da yara ƙanana suka koma marayu.
Lura da da cewa babu takamaiman sansanonin ’yan gudun hijira da gwamnati ta amince da su a wasu jihohin Arewa-maso-Yamman, wadanda ta’addancin ’yan fashin ya shafa, sun ce ba su da zabi illa su yi hijira zuwa wuraren masu tsaro kamar Abuja.
Sai dai jim kaɗan bayan sun samu mafaka a Abuja, galibinsu sun tsinci kansu tamkar a yanayin gudun gara a tarar da zago, yayin da suka fara fuskantar sababbin ƙalubale biyo bayan matakin da hukumar raya birnin Abuja ta ɗauka na kakkaɓe birnin daga gajiyayyu da mabarata.
Idan ba a manta ba, a watan Oktobar 2024 ne Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya umarci mabarata da su fice daga birnin ko kuma a kama su. Ministan ya yi tir da tururuwar mabarata da gajiyayyun, yana mai alakanta yawaitar gajiyayyun da ɓata-garin da ke sajewa ciklinsu, suna aikata miyagun laifuka da sunan barace-barace, wanda hakan a cewarsa ya sa aikin samar da tsaro a Abuja yake zama da wahala.
Wike ya ce, korar na daga cikin dabarun gwamnatin na dawo da martabar Abuja da kuma tabbatar da cewa birnin ya yi gogayya da sauran manyan biranen duniya.
Duk da cewa ’yan gudun hijirar sun bijire wa matakin, bisa dalilin cewa, bara ba ita ce rayuwar da suka zaɓa wa kansu ba, amma hukumomin Abujan sun yi kunnen uwar shegu da hanzarin mabaratan.
Rundunar haɗin gwiwa da ta kunshi ’yan sanda da sojoji da jami’an tsaron farin kaya da sauran jami’an tsaro ne suka gudanar da farmakin, inda a farkon farmakin sun yi kame a manyan wurare hudu: kwaryar birnin Abuja da hanyar zuwa tashar jiragen sama da yankin Kubwa zuwa Gwarinpa da kuma unguwannin Asokoro-Nyanya-Karu. Daga baya aka fadada shi zuwa sauran yankunan.
Kwamishinan ’yan sanda na Abuja, Olatunji Disu ya bayyana dakatarwar a matsayin “aikin kasa,” inda ya umurci jami’an da su aiwatar da aikin cikin himma da kwarewa.
Aminiya ta ruwaito cewa, bayan aikin da ya kakkaɓe su daga birnin Abujan, ’yan gudun hijirar sun koma wasu garuruwan Jihar Nasarawa, wadanda ke kusa da Abuja maimakon komawa jihohinsu.
Kodayake akan samu wasu mabaratan da suke sulalowa su shiga Abuja, suna bara da rana sannan su koma bayan gari zuwa yamma. Duk da haka, suna wasan buya da jami’an tsaro, inda hukumomin tsaron suke korar su daga kwaryar birnin Abuja da Kasuwar Wuse da Berger da unguwannin Utako da Jabi da sauran wurare a cikin birnin Abujan.
Wani babban jami’i a rundunar da ya nemi a sakaya sunansa saboda ba a ba shi damar yin magana da manema labarai ya ce, sama da mabarata 300 da sauran gajiyayyu ne aka kwashe daga titunan Abuja a lokacin aikin na baya-bayan nan.
Ya ce, wasu daga cikinsu an kai su Cibiyar Gyaran Tarbiyya ta Abuja da ke Kuzhako a karamar Hukumar Bwari ta Abuja, yayin da wasu kuma aka mai da su jihohinsu na asali.
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa mabaratan suke samun damar komawa birnin Abuja makwanni kadan bayan aikin kakkabe sun, sai ya ce, “abin da yake faruwa shi ne, wasu daga cikinsu sun fice zuwa wurare kamar Mararaba a Jihar Nasarawa, wanda ke kusa da babban birnin tarayya Abuja. Suna zuwa Abuja, su yi bara da rana, sannan su koma da daddare. Ba wai hakan yana nufin aikin ya samu tasgaro ba ne. Aiki ne da zai ci gaba da gudana, har yanzu za mu ci gaba da fatattakar su,” in ji shi.
Galibinsu daga Katsina suka fito
Aminiya ta gano cewa, galibin ’yan gudun hijirar al’ummomi ne da tashetashen hankula da ’yan bindiga suka daidaita, inda miliyoyin mutane suka rasa muhallansu na tsawon lokaci.
Daga Jihar Katsina misali, ’yan gudun hijirar sun fito ne daga kananan hukumomin Faskari da Malumfashi da Bakori da sauran kananan hukumomin jihar da matsalolin tsaro suka yi wa dabaibayi.
Mabaratan wadanda galibinsu mata ne da kananan yara, sun bayyana cewa, sun shiga cikin wannan mawuyacin hali ne sakamakon yawaitar tashe-tashen hankula da ’yan bindigar suka jefa su ciki, wadanda aka fi sani da ’yan fashin daji.
Tashe-tashen hankulan ba kawai dagula musu rayuwarsu ya yi ba, har ma da jawo asarar rayukan mazajensu da iyayensu, inda hakan ya sa galibinsu suka rasa tudun dafawa domin biyan bukatun yau da kullum.
Da suka zanta da Aminiya a garin Mararaba na Jihar Nasarawa sun ce, karuwar matsin lamba daga hukumomin Babban Birnin Tarayya – Abuja kan mabarata da gajiyayyu ya tilasta musu neman mafaka a garuruwan Jihar Nasarawa da ke kusa da Abuja.
Garuruwa kamar su Keffi da Mararaba da Karu da Uke da Ado za a iya cewa sun zama tudun mun tsira ga wadannan mabaratan da sauran gajiyayyu.
Abubuwan da suka ci koro da su
A wata ziyarar da Aminiya ta kai wa wasu daga cikin wuraren da suke zama, wakilinmu ya ce, sun samu kansu a halin gaba kura baya sa yaki, lura da yadda rayuwa ta zama mai wahala a wajensu.
Yayin da wasu mazauna yankin suke musu kallon wata matsala a wasu yankunan, su kuwa jami’an tsaro fatattakar suke a koyaushe. Sai dai wasu daga marabatan da uka samu mafaka a sansanonin ’yan gudun hijira da Gwamnatin Tarayya ta samar, wasu kuma suna kwana a karkashin gadoji da kasuwanni da kantuna.
‘Sun kona mijina da ’yata’
Wata mata mai suna Yaha, ta bayyana yadda ’yan bindigar suka bindige mijinta tare da ’yarsu.
Matar wacce har yanzu take faman yadda za ta ci gaba da rayuwarta, da kyar ta yi magana lokacin da aka yi mata wasu tambayoyi.
“Ba na so in tuna wannan mummunar ranar … Ba na son ba da labarin ga kowa. Duk da cewa abu ne da ba zan taba mantawa da shi ba, ba na fatan wani ya tsinci kansa a irin yanayin dimuwa da na shiga ciki,” inji ta.
Da aka tambaye ta ko za ta bayyana yadda aka kashe iyalan nata, sai ta ce, “kai dai bari, ku yi mana addu’a kawai, mu ma mutane ne kuma muna son rayuwa cikin mutunci da kamala. Ba haka muka so rayuwar ta kasance mana ba,” in ji ta.
‘Yan bindiga sun kashe mijina’
Baba Asabe, uwa ce mai ’ya’ya uku da ta rasa mijinta a harin da ’yan bindiga suka kai a karamar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina ta ce, rayuwa ta matukar sauyawa mata tun bayan rasa mijin nata.
Ta ce, an sace babban danta mai shekara 20 sannan sau biyu danginta suna tara kudin fansa domin a sako shi daga hannun masu garkuwar da suka yi awon gaba da shi.
Baba Asabe ta kara da cewa, sai da ta yi kaura daga karkarar zuwa wani wajen saboda kutsen da ’yan fashin dajin ke yi. Ta ce, duba da cewa babu sansanin ’yan gudun hijira a garin Katsina ko a karamar Hukumar ta Bakori, sai aka ba ta shawarar yin hijira zuwa Abuja, inda ta sai ta yi bara kafin ta samu na abinci.
“Amma na takaita yawon barata zuwa nan yankin Maraba kawai, bayan an kama ni sau biyu. Ba na son a sake kama ni.”
Ta kara da cewa, “a lokacin da aka kama ni na farko a Abuja, sai da na biya Naira dubu 10 kafin a sake ni. Na kuma biya Naira dubu 13 ita ma a matsayin tara kafin a sako ni, bayan da aka kama ni a karo na biyu ke nan. Yanzu, ina bara a nan Mararaba.”
“Da kyar muke samun ciyar da kanmu da siyan wasu muhimman abubuwa na rayuwar yau da kullum, kamar su wanka da sabulun wanka. Akwai lokutan da za ka samu kudi daga Naira dubu biyu zuwa dubu biyu da dari biyar, amma wani lokacin da kyar za ka samu Naira dubu da dari biyar ma. Muna fara bara daga karfe 7 na safe sannan mu dawo da faduwar rana. Ina cikin kwanciyar hankali a nan.
“Can a gida – kauye ke nan, karar harbe-harben bindigogi ya zama ruwan dare. Kuna zaune haka kawai, ’yan fashi za su mamaye ku, su sace mutane,” in ji ta.
Asabe ta ce, kullum addu’ar Allah Ya dawo da zaman lafiya a yankunan take yi, ta yadda za ta koma gida.
“Ni ’yar Kakumi ce. Akwai lokacin da na ziyarci gida, amma bayan kwana daya kawai ala tilas na dawo nan Abuja. ‘Yan bindiga sun yi wa kauyenmu kawanya, inda suka ci karensu babu babbaka,” in ji ta.
Ita ma Habi Garba mai shekara 60 ta bayyana irin wannan labari: “Ni ’yar Kakumi ce a karamar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina. Ina da ’ya’ya da na baro a can Katsina. Na bar garinmu kimanin wata uku da suka wuce. daya daga cikin ’ya’yana da ya manyanta ya rasa matarsa, ta bar ni da jikoki.”
“Ni kadai ce a nan ina barar abin da zan ci, n ci gaba da rayuwa. Duk lokacin da ’yan fashin suka kawo hari a kauyukanmu, mukan gudu, mu zo nan. Sun kashe kusan mutane biyar a ranar da muka gudu. Suna cutar da mu, suna gallaza mana a garuruwanmu. Sun kwashe dukiyoyinmu da kudi da dabbobi.
“Sun hana mu noma. Ba ku ji cewa farashin dawa ya karu ba? Yunwa tana yi wa mutane illa. Rayuwa ta yi tsanani sannan rayuka da dama sun salwanta.
“Ba mu kasance mabarata a baya ba sai yanzu. Ina da yara kanana, wasu kuma sun yi aure. Ina yin barar domin ba ni da wani zabi. Ba na jin dadin hakan. Ina so in daina bara, na gaji da ita. Ina so in koma in zauna a karkarata, amma ’yan fashi suna ta’asa a wuraren ta yadda ba ma iya shiga wajen,” in ji ta.
“Na daina shiga Abuja domin bara saboda fargabar za a kama ni. A nan muke bararmu. Akwai masu gadin mu a nan, musamman da dare. Suna kula da mu yadda ya kamata saboda suna gadin shaguna da kasuwar nan,” a cewarta.
Ita ma kamar Habi Garba, Halima Hamza ta yi hijira zuwa Abuja domin ta kula da iyalinta sannan ta tara kudin aurar da diyarta mai shekara 18, wacce take tare da ita a garin na Mararaba.
“Ni ’yar Runka ce. ‘Ya’yana takwas, amma biyu sun rasu. Da farko na baro su a gida, amma da barayin dajin suka tsananta kai hare-hare a kauyenmu, sai na koma, na dauko kanana guda biyu cikinsu na kawo su nan. Guda na sa ta a makarantar allo ta dare. daya daga cikin ’ya’yana yana Legas, wadanda suka yi aure kuma suna can gida Katsina.
“Akwai lokacin da barayin suka yi garkuwa da mutum kimanin 37 sai da aka biya Naira miliyan 25 kafin a sako su bayan sun shafe wajen wata biyar a daji,” in ji ta.
A cewar Halima, gabanin tsautsayin aika-aikar barayin dajin ta tilasta musu hijira, ta kasance tana kananan sana’o’i domin samun rufin asiri.
“Jarin ya karye aka biyo ni bashin Naira dubu 250. Dalilin ke nan da na zo nan ina bara. Ina nan ina ta biyan bashin. Akwai sauran dubu 15. Da zarar na kammala biyan bashin kuma na dan tara abin da zan saya wa ’yata kayan daki, zan koma gida. Saboda mun ji an ce sannu a hankali zaman lafiya ya fara samuwa. Zan kuma mayar da yarana zuwa makaranta.”
Yayin da Hassana Amiru take bara, yaranta kuwa da ke tare da ita a garin Mararaba, suna sana’ar sayar da fiya wata da biskit da sauran kayayyaki.
“Na taho daga yankin Mashi na Jihar Katsina. Ina da yara a can. Babban shekararsa 15 dayan kuma shekara 10. Ni ce babba a nan, don haka ni ce tamkar shugabarsu. A nan muke kwana karkashin gadar Mararaba.
“Masu shaguna a nan sukan ba mu wajen kwanciya da dare. Akwai wajen wanka da bahaya a nan kusa, inda muke zuwa, mu biya bukata.
“Galibin matan nan daga Batsari da Faskari da sauran wuraren da rashin tsaro ya yi kamari suka fito a jihohin Katsina da Zamfara.
“Mukan je ganin gida jefi-jefi. Mukan fita bara daga karfe 10 na safe sannan mu dawo da yamma daidai sallar Magariba. Da zarar mun samu na abinci sai mu gode wa Allah, mu dawo nan.
“Ina tare da yarana a nan. Ba sa zuwa makaranta, amma suna son shiga makarantar boko in dama ta samu. Na aurar da wasu daga cikin ’ya’yana mata,” in ji ta.
Shi kuwa Ahmad Salisu, matashi mai shekara 20, wanda kafin zuwan sa Abuja yake sana’ar gyaran waya a kauyensa da ke Jihar Katsina – gabanin matsalar tsaro ta samu gindin zama.
“Kusan shekara guda ke nan nake bara a nan Mararaba. Da nakan shiga birnin Abuja ina bara a unguwanni irin su Maitama, amma an taba kama ni sau daya, inda na kwashe wuni biyu a tsare, ga shi ba abinci a wajen da dai sauran kalubale.
Ƙarin rahotanni daga Yusha’u A. Ibrahim, (Zamfara) da Tijjani Ibrahim (Katsina) da Abubakar Auwal (Sakkwato)