Girke-girken Azumi: Yadda ake yin Tsiren Dankali
Yau a filin namu na Girke-girken Azumi za mu kawo muku yadda ake yin Tsiren Dankali.
Yau a filin namu na Girke-girken Azumi za mu kawo muku yadda ake yin Tsiren Dankali.
Za a iya amfani da girkin namu na yau a matsayin abin buda-baki, da zarar an sha ruwa.
Ga kayan hadin da ake bukata don yin girkin:
Dankali Turawa
Nikakken nama
Man gyada
Sinadarin dandano
Kori
Tyme
Tafarnuwa
Tsiken tsire
Yadda ake hada shi
A samu nikakakken nama sai a hada da kayan kamshi(kori, tyme da tafarnuwa) da sinadarin dandono.
Idan ya hadu sai a gutsira a fadada shi yadda zai yi falan-falan sai a ajiye shi a gefe.
Sannan a dauko dankali sai a fere shi, a yayyanka shi kamar kwabo.
Sai a dauko tsinken tsire a jera dankalin a jiki tare da hadadden nikakken naman.
Idan an sa dankali a jikin tsinken sai a dauko wannan nikakken naman a sa shi a jiki daidai fadin dankalin sannan sai a sake sa dankalin sai a sa naman.
Haka za a yi, har sai tsinken ya cika.
Amma a tabbatar dankalin da aka yanka ya kasance guda daya, ma’ana sai kin gama da guda daya, sannan za a sake yanka wani don kada ya hargitse wajen dankalin a jikin tsinken.