Yadda ake yin ‘doughnut’
Assalamualaikum! A yau nazo muku da yadda ake hada doughnut cikin sauki. Doughnut abun ci ne ake yi da fulawa da sauran kayan hadi domin marmari, tarbar baki, ko sana’a. Kayan hadi: Fulawa kofi 2 Gishiri cokali 2 Sukari kofi 1 Kwai 2 Bota cokali 2 Yis cokali 2 Ruwa rabin kofi Yadda ake […]
Assalamualaikum! A yau nazo muku da yadda ake hada doughnut cikin sauki.
Doughnut abun ci ne ake yi da fulawa da sauran kayan hadi domin marmari, tarbar baki, ko sana’a.
- Kayan hadi:
- Fulawa kofi 2
- Gishiri cokali 2
- Sukari kofi 1
- Kwai 2
- Bota cokali 2
- Yis cokali 2
- Ruwa rabin kofi
- Yadda ake hadawa
- Da farko za a sa ruwan dumi cikin kofi daya da rabi sannan a zuba yis da sukari a ciki.
- A rufe ruwan a ajiye shi na tsawon mintoci 15.
- A zuba fulawa, sukari da gishiri a kwano, sannan a fasa kwai a ciki.
- Daga nan sai a kawo hadin yis din a zuba a kai.
- Sai a sa bota a buga shi sosai saboda doughnut na bukatar bugawa sosai.
- Bayan haka sai a rufe a ajiye shi a wuri mai dumi.
- Idan ya tashi sai a sake bugawa a fitar da fasalin da aka bukata a bar shi na tsawon mintoci 15.
- Daga nan kuma sai a fara soyawa.
Yadda ake doughnut ke nan a cikin sauki.