Yadda ake fanken ayaba
Yadda ake fanken ayaba (Banana balls)
Jama’a Assalamu Alaikum, yaya azumi. Yau kuma mun kawo muku yadda ake yin fanken ayaba, wato Banana balls a Turance.
Amma kafin mu shiga ka’in da na’in, ga abubuwan hadin da ake bukata:
– Ayaba
– Fulawa
– Kwai
– Madara
– Sukari
– Baking powder
– Yis
– Ruwa
– Man gyada
- Za mu ci gaba da ragargazar ’yan ta’adda —Babban Hafsan Sojojin Kasa
- Kotu ta sake aike wa Rarara sammaci saboda taurin bashi
Yadda ake hadawa
– A tankade fulawa da baking powder a cikin kwano mai zurfi, a zuba madara da sukari sannan a fasa kwai a ciki
– A yayyanka ayaba kanana a zuba a ciki sannan a kwaba sai ya hadu sosai
– Sai a zuba yis da ruwa, a sake kwabawa sosai har sai ya yi kauri kamar kullun fanke
– A rufe kamar na minti 30 ko fiye da haka
– Sai a dora tukunya a wuta a zuba man gyada
– Idan man ya yi zafi sosai sai a rika jefa kullin a ciki ana soyawa kamar fanke
– Idan ya soyu sosai sai a kwashe
– A barbada sukari a kan soyayyen fanken
Ana iya ci da shayi ko da duk wani lemon sha.