Yadda ake yin masar dankalin Turawa

Barkanmu da sake saduwa da ku Uwargida. Yaya yara? A yau na kawo muku yadda ake hada masar dankalin Turawa domin yin abin karyawa. Tare da fatan za a gwada irin wadannan girke-girken da muke kawo muku. A sha karatu lafiya. Abubuwan da za’a bukata •        Dankalin Turawa •        […]

Yadda ake yin masar dankalin Turawa

Barkanmu da sake saduwa da ku Uwargida. Yaya yara? A yau na kawo muku yadda ake hada masar dankalin Turawa domin yin abin karyawa. Tare da fatan za a gwada irin wadannan girke-girken da muke kawo muku. A sha karatu lafiya.

Abubuwan da za’a bukata

•        Dankalin Turawa

•        Attarugu

•        Albasa

•        kwai

•        Gishiri da magi

•        Kori

Hadi

Bayan uwargida ta fere dankalinta, sai ta dora shi a wuta ya nuna ya yi luguf sosai. Sannan sai ta dauko roba ko kwano mai zurfi ta zuba a ciki. Sai uwargida ta debo kwai mai dan dama ta fasa a kan dankalin. Sai ta samu ludayinta ta dama dankalin da kwan har sai sun hadu sosai.

Sai a debo albasa da attarugu a jajjaga su sannan a zuba a kan hadin dankalin da magi da gishiri da kori daidai dandano sannan sai a sake dama hadin domin kayan hadin su shiga dankalin sosai.

Idan uwargida ta gama hakan, sai ta dauko tanda ta dora a kan wuta. A zuba man gyada a kowane gida sannan a debo kullun dankalin a zuba a kowane gidan tandar. Sai a dan ba shi mintuna domin dahuwar cikin masar. Idan gefe daya ya yi, sai a sake juya wainar zuwa dayan gefen har sai ta nuna kafin a sauke daga wuta.

Himn! Za a iya yin wannan girki a wannan wata domin samun ladan maigida ko kuwa yi wa wadanda suka zo shan ruwa a gidanki.