Yadda ake yin miyar zogale

Zogale na dauke da muhimman sunadarai, yana kuma da amfani a matsayin abinci da magani.

Yadda ake yin miyar zogale

Zogale abinci ne mai matukar amfani a jiki, wanda ake sarraffa shi ta hanyoyi daban-daban kamar kwado, miya, magani da dai sauransu.

Shi ya sa a wannan karon muka yi wa uwar gida tsarabar yadda ake yin miyar zogale, wadda ana iya cin ta da sakwaro ko tuwo.

Kayan miya

  1. Zogale
  2. Nama
  3. Sunadarin dandano
  4. Albasa
  5. Gyada
  6. Citta
  7. Tafarnuwa

Yadda ake hadawa

Da farko za a wanke naman a sa albasa da sunadarin dandano a dora a wuta ya tafasa sosai.

Sai a gyara zogalen a ajiye a gefe, a jajjege attarugu da alabasa da tafarnuwa da citta a ajiye a gefe.

Idan naman da ya yi sai a zuba jajjaggen attarugun a tsayar da ruwan miya.

Daga nan sai a sanya gishiri da sinadarin dandano a rufe ya yi kamar minti biyar.

Idan ya yi sai a zuba zogale a rufe, shi ma ya samu kamar minti biyar.

Bayan nan sai a zuba gyada a rufe, idan ya nuna  sai ki sauke.

Dabarun girki

Ga wasu dabarun girki da uwar gida za ta iya amfani da su:

  • Kafin a bare bayan albasa a saka ta a cikin firinji ta yi sanyi, hakan zai hana ta yi yaji idan nan yankawa.
  • Bayan a fere dankali a sa a cikin ruwan sanyi domin kar ya sauka launi

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos