Yadda ake yin Wainar Dankali
Kayan hadi: . Dankalin Hausa . Kwai . Hoda da yis . Attarugu da albasa . Kayan kanshi . Man gyada Yadda ake yi Da farko uwargida za ki dafa dankalinki na Turawa ko na Hausa sai ki sami kwano ki juye shi sai ki sa cokali ki farfasa shi yadda zai yi laushi. Sai […]
Kayan hadi:
. Dankalin Hausa
. Kwai
. Hoda da yis
. Attarugu da albasa
. Kayan kanshi
. Man gyada
Yadda ake yi
Da farko uwargida za ki dafa dankalinki na Turawa ko na Hausa sai ki
sami kwano ki juye shi sai ki sa cokali ki farfasa shi yadda zai yi
laushi. Sai ki kawo kwai ki fasa a kai, sannan ki kawo kayan kanshi da
suka hada da citta da kirfa da tafarnuwa da sauran kayan kanshi. Sai
ki kawo sinadarin dandano ki zuba a ciki sannan ki kawo jajjagaggen
attarugu da yankakkiyar albasa mai yawa ki zuba a ciki sai ki juya,
yadda zai hadu sosai. Idan ya hadu sai ki kawo bakar hoda da yis ki
zuba a ciki domin ya tashi. Sa ki rufe. Sannan sai ki dauko tandarki,
ki dora akan wuta ki zuba mai a ciki. Sai ki rika diban wanann hadin
dankalin kina zubawa a ciki. Ki lura idan kwabin ya yi kauri sai ki
dan kara ruwa amma kada yayi yawa. Daga nan sai ki fara soyawa kamar
yadda ake soya wainarki.
Ana iya cin wannan dankali da miyar nikakken nama ko a ci ta da lemo ko shayi.
Kwalliya