Yadda ake yin ‘yam balls’ a saukake

Matakan yadda ake yin kwallon doya da kwai cikin sauki

Yadda ake yin ‘yam balls’ a saukake

Jama’a barkan mu da wannan lokaci, a yau za mu nuna yadda ake yin kwallon doya da kywai (yam balls) a gida a saukake.

Ana iya yin ‘yam balls’ a matsayin abinci don marmari, tarbar baki ko sana’a.

  1. Doya
  2. Attarugu
  3. Albasa
  4. Kwai
  5. Magi
  6. Gishiri
  7. Kori
  8. Mai
‘Yam balls’ a cikin faranti
  • Yadda ake hadawa
  1. Da farko za a fere doya a yanka ta sai a wanke a sa a tukunya a dora a wuta da dan gishiri a bari ta nuna.
  2. Idan ya nuna sai a sauke a kawo turmi mai tsafta a daka doyar sama sama.
  3. Sai a dauko jajjagen attarugu, albasa, magi da kori a zuba a kan doyar a juya su hadu sosai.
  4. Daga nan sai a rika dunkula doyar a yi ta kamar kwallo.
  5. Sai a fasa kwai a dora kasko a wuta a sa mai.
  6. Idan man ya yi zafi sai a rika dauko kwallon doyar ana sawa a kwai ana soyawa a man.
  7. Idan ya yi sai a kwashe.

Yadda ake yin yam balls ke nan, da fatan za a jaraba a gani.