Yadda ake zaman ɗarɗar saboda rushewar gidaje a Kano
Duk lokacin da aka yi ruwa unguwanninmu cika suke yi wani wajen ma za ka iya sa kwale-kwale ka yi tafiya a ciki.
Mazauna unguwar Ƙofar Mata da ke ƙwaryar birnin Kano sun ce suna rayuwa cikin fargaba a dalilin rushewar gidaje da aka samu a bayan nan.
Hakan ya biyo bayan mamakon ruwan sama da aka samu a ranar Juma’ar da ta gabata da ya janyo rushewar aƙalla gidaje 13 tare da kuma ajalin mutum ɗaya da jikkatar wasu da dama.
- Mutanen gari sun kama mai garkuwa da mutane a Jos
- An ba masu tsoffin gidaje kwana 7 su fice a Ibadan
Aminiya ta ziyarci unguwar ta Ƙofar Mata inda ɗaruruwan magidanta da iyalansu suka bayyana fargabarsu duba da yadda rushewar gidajen ke barazana ga rayukansu.
A ranar Asabar da ta gabata ce mazauna unguwar suka wayi gari da mummunan labari na rasuwar wata mata mai suna Maman Abba.
Aminiya ta samu rahoton cewa matar ta rasu a ɗakinta bayan da gini ya rufta kanfa ana tsaka da ruwan sama tare da jikkatar wata jikarta da suke kwana tare a ɗakin.
Wata mata mai suna Baba Larai wacce ’yar uwa ce ga marigayyar, ta labarta wa Aminiya yadda lamarin ya faru.
A cewar Baba Larai, “A ranar Asabar ana ruwa aka yi wata tsawa mai ƙarfi, to tun daga sannan ni ma da na tashi ban koma barci ba.
“Ina ta salati cikin ikon Allah bayan wannan tsawar ba a yi minti goma sha biyar ba ginin wannan ɗaki ya faɗo mata ita da jikarta suna kwance.
“Ita jikar ta sako kanta daga waje ita kuma marigayiyar tana daga ciki, to a nan ƙasar da ta zuba ta danne ta [marigayiyar] ita kuma jikar wasu bulo da azara suka faɗo suka tsaga mata kai sai da aka yi mata ɗinki.
Baba Larai ta ci gaba da cewa, “ƙurar da ta [marigariyar] shaƙa ya sanya numfashinta sassarƙewa da ƙyar aka gano ta saboda ƙasa ta rufe ta duka sannan aka ɗauko ta a hannu kafin a ƙarasa asibiti ma ta rasu.
Larai ta ƙara da cewa saboda tsananin tashin hankali da fargabar da ta shiga a wannan rana har sai da ta ta rasa gane hanyar fita daga gidan.
“Kawai sai ji mu ka yi an zo ana ta dukan ƙofar gidanmu. Muka tashi muka ce lafiya na ma rasa gane hanyar fita waje. Sai mai gidana ne ya fito ya ce lafiya suka ce ɗaki ne ya faɗa wa su Maman Abba. Shi ne aka tafi asibiti kuma babu jimawa suka dawo aka ce ta rasu.
“Da ma mu uku ne sai ɗan autarmu. To yanzu ita ta mutu sai ni da mai bi na sai ɗan autarmu sai yaranta da ta bari guda bakwai,” inji Larai.
Ita ma wata mata A’isha Yahaya Gidan Shayi ta tsallake rijiya da baya ita da ’ya’yanta da asubahin wannan ranar yayin da benen da suke ciki ya rufta.
“Muna kwance bayan Asuba sai cikin hukuncin Allah muka ji abu yana ‘ƙas ‘ƙas.
“Ina leƙawa sai gani na yi baranda ta yi ktasa wasu yara suna ihu. Sai na ce ku daina ihu ku yi ta faɗin innalilLahi wa inna ilaiHi raji’un domin na saddaƙar cewa mun mutu.
“Sai wata yarinyata ta rugo da gudu sai na janyo ta baya cikin tashin hankali yaran suna ta faɗin ‘mun mutu umma’, na ce ba mu mutu ba kowa hankalisa ya tashi.
“Sannan na sa aka saukar da su ƙasa sai ya rage daga ni sai wata mata ’yar hayar gidammu ita ma sai ihu take.
“Katangar da ke gefenmu ta yanko ta faɗo amma cikin hukuncin Allah ba ta sami kowa ba. To tun daga wannan Allah bai sa wani gurin ya sake faɗowa ba.
Gidajen 13 wanda ya haɗa da gidan Balaraba Yahaya da Aisha Yunusa da Zainab Muhammad da Usman Bello Kofar Mata da wasu da dama da wannan ibtilai ya rutsa da su
A cewar Alhaji Muhammad Jibrin Mai Unguwar Ƙofar Mata, har kawo yanzu mahukunta ba su magantu a kan wannan al’amari ba.
“To har yanzu dai ba wani abu da hukuma ta yi a kai amma mu a cikin unguwa tun ma kafin faɗuwar damina an sami haɗin kai na matasa an yi gyare-gyaren kwatoci da yashe magudanan ruwa.
“Amma har yanzu hukuma babu wani abu da ta yi mana kuma duk lokacin da aka yi ruwa unguwanninmu cika suke yi wani wajen ma za ka iya sa kwale-kwale ka yi tafiya a ciki.
Mai unguwar ya yi kira ga gwamnati da ta kawo musu ɗauki akan wannan ibtila’i da suke fuskanta.
“Muna kira ga gwamnati musamman ta ƙaramar hukuma da a shigo a taimaka mana kan wannan ibtila’i da yake damunmu.”