Yadda ake zaman jiran ci gaban Shari’ar Masarautar Kano a kotu

An hallara a Babbar Kotun Tarayya da ke Gyadi-gyadi don ci gaba da sauraron shari’ar Rikicin Masarautar Kano

Yadda ake zaman jiran ci gaban Shari’ar Masarautar Kano a kotu

A Alhamis din nan Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano za ta ci gaba da zaman sauraron shari’ar da ke gabanta kan Rikicin Masarautar Kano.

Aminiya  ta ruwaito cewa a halin da ake ciki an girke jami’an tsaro a zagaye da hanyar zuwa kotun kuma jama’a da manema labarai suna zaman jiran isowar alkalai da lauyoyi bangaren Sarki Aminu Ado Bayero da bangaren Sarki Muhammadu Sanusi II.

Za a gudanar da zaman ne bayan da farko ya kasa yiwuwa a ranar Litinin sakamakon yajin aiki da kungiyar ta fara kafin daga bisani ta janye washegari.

Aminiya  ta ruwaita a ranar Litinin cewa duk da cewa Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya zo domin zaman, amma jami’an kungiyar kwadago sun kulle harabar sun hana shiga kotun.

Daga bisani wani jami’in kotun da ya nemi a boye sunansa ya sanar cewa an dage zaman saboda yajin aikin, ya kuma musanta yiwuwar gudanar da zaman  kotun ta intanet ta kafar Zoom.

Mako biyu ke nan da da ake kai ruwa rana a Kano bayan majalisar dokokin jihar ta yi gyaran fuska ga dokar masarautun jihar.

A ranar Alhamis  26 ga watan Mayu ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sa hannu kan sabuwar dokar da ta soke duk sabbin masarautun jihar guda biyar da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro.

Bayan nan ne aka naɗa Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano bayan tube Sarki Aminu Ado Bayero.

A kan wannan lamari ne Sarki Dawaki Babba, Alhaji Animu Baffa Danagundi ya je gaban kuliya, inda Babbar Kotun Tarayya ta hana nada Sarki Sanusi II.

Daga bisani Babbar Kotun Jihar Kano ta hana Sarki Aminu ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano, wanda bayan nan Gwamna Abba ya ba da umarnin a kama shi.

Bayan haka ne Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin kama Sarki Sanusi II.

Ana iya tuna cewa a makon jiya Shugaban Alkalan Najeriya ya gayyaci shugaban kotun da takwaransa na Babbar Kotun Jihar Kano kan umarnin da suka bayar masu karo da juna kan shari’ar Sarautar Kano mai cike da rudani.