Yadda ake zuwa ta’aziyyar mahaifin Kwankwaso a Kano
Shugaba Buhari da Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje sun aike da sakon gaisuwarsu ga tsohon gwamnan.
A ranar Juma’a ne 25 ga Disamba 2020, aka binne mahaifin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon Gwamnan Kano a gidansa da ke Kano.
Mutane da dama sun aike da sakon ta’aziyyarsu zuwa ga Sanata Kwankwaso bisa rasuwan mahaifin nasa.
- Buhari ya jajanta wa Kwankwaso, ya taya Ganduje murna
- Yadda aka yi jana’izar mahaifin Kwankwaso a Kano
- Abba Gida-Gida ya yi alhinin mutuwar mahaifin Kwankwaso
- Ganduje ya yi wa Kwankwaso ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa
Ciki har da gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Mataimakin Gwamna a zamanin Kwankwason.
Daga cikin wanda suka halarci jana’izar, akwai tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido, da fitattun ’yan siyasan Kano, irinsu Alhaji Murtala Sule Garo, Kawu Sumaila, Aminu Dabo, A.Y Maikifi, Shugaban PDP na Kano, Shehu Wada Sagagi, Musa Iliyasu Kwankwaso da sauransu.
Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari shi ma ya aike da sakon gaisuwarsa na rashin da Sanata Kwankwaso ya yi.
Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila shi ma ya jajanta wa tsohon gwamnan.
A ci gaba da karbar gaisuwar, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya shi ma ya ziyarci Kwankwaso, inda yaje yi masa ta’aziyya.