Yadda Allah Ya yi ni Malamar Makaranta – Hajiya Habiba Aliyu Barau

Hajiya Habiba Aliyu Barau tsohuwar Malamar Makaranta ce daga Jihar Neja. An haife ta shekara 56 da suka gabata a iyalan wani jami’in soja, Ibrahim Pindiga da kuma Malama Asabe Ibrahim da aka haife su su biyar. A yanzu ita ce Mataimakiyar Daraktan Sashen Hada Hannun Tsakanin Gwamnati da Cibiyoyi Masu Zaman Kansu (PPP) a […]

Yadda Allah Ya yi ni Malamar Makaranta – Hajiya Habiba Aliyu Barau

Hajiya Habiba Aliyu Barau

Hajiya Habiba Aliyu Barau tsohuwar Malamar Makaranta ce daga Jihar Neja. An haife ta shekara 56 da suka gabata a iyalan wani jami’in soja, Ibrahim Pindiga da kuma Malama Asabe Ibrahim da aka haife su su biyar. A yanzu ita ce Mataimakiyar Daraktan Sashen Hada Hannun Tsakanin Gwamnati da Cibiyoyi Masu Zaman Kansu (PPP) a Hukumar Ilimin Bai-Daya ta Kasa (UBEC).  Ta bayyana wa Aminiya yadda rayuwarta ta taso:

Ilimi

An sanya ni a Makarantar Firamare ta Saint Micheal da ke  Minna, wacce yanzu ake kira da Makarantar Firamare ta Waziri. Daga nan na wuce Kwalejin Horar da Malamai Mata (WTC) ta Jihar Neja. Daga nan kuma sai na wuce Kwalejin Ilimi (COE) da ke Minna inda na karanci Harshen Ingilishi da Kimiyyar Rayuwa inda na gama a 1984. Daga nan kuma sai na wuce Abuja inda na shiga Jami’ar Abuja na yi digirina na farko a fannin Tsimi da Tanadi a shekarar 2001.

Aiki

Wadansu mutane Allah Ya yi su ne domin su karantar, kuma ni daya ce daga cikinsu. Na fara karantarwa ce tun ina Kwalejin Horar da Malamai Mata, tunda ka san cewa dole sai ka yi aikin koyarwa na samun horo kafin ka gama wannan makaranta. Saboda haka na je irin wannan aiki na farko ne tun a 1981 inda daga baya na kammala wannan makaranta a 1982. Bayan na gama sai kuma na fara aikin koyarwa a makarantar firamaren da na yi ta Waziri Firamare. A lokacin da na gama Kwalejin Ilimi kuma sai na wuce Abuja tare da mijina inda na fara aiki a can a 1990. Na fara aikin koyarwa a Makarantar Firamare ta Unguwar Eriya Wan da ke Garki, inda na yi aiki na shekara bakwai a can. Na samu mukamin Mataimakiyar Hedimasatan makarantar daga 1997 zuwa shekarar 2002.

Daga bisani kuma sai aka mayar da ni Makarantar Firamare ta Kado inda na zama Shugabar Makarantar ta farko. Na yi aiki na shekara biyu a wurin sai tsohon Minsitan Abuja Malam Nasir El-Rufa’i ya bayar da umarnin mayar da kula da makarantun a karkashin kulawar Hukumar Ilimi ta Babban Birnin Tarayya. Don haka ina daya daga cikin shugabannin makarantun firamare da aka dauka inda aka tura ni Makarantar Firamare ta Gwaji (Model) ta Asokoro a cikin shekarar 2005. Ban jima sosai ba aka mayar da ni Makarantar Firamare ta Barikin Soja na Mogadishu inda na yi aiki daga shekarar 2006 zuwa 2008, sai kuma aka mayar da ni zuwa Makarantar Firamare ta Jabi a can ma na shafe shekara biyu ina aiki. Canjin da aka yi mini na karshe shi ne zuwa Makarantar Firamare ta Nyanya inda na zauna a can daga shekarar  2010 zuwa 2012.

A lokacin da aka yi mini Mataimakiyar Darakata sai aka tura ni a sashin tabbatar da inganci (Kuality Insurance) kuma aka ce in shugabanci wannan wuri, hakan kuwa na yi na shekara daya wato daga 2013 zuwa 2014. Daga nan kuma sai aka tura ni zuwa LEA Municipal Office a matsayin shugabar Bangare a cikin wannan wata dai aka kara min girma na zama Shugabar Sashe (HOD).  Don haka na kasance shugabar ayyukan makarantu na Karamar Hukumar Birnin Abuja (AMAC)  daga 2015 zuwa yanzu da aka mayar da ni Babban Ofishin Hukumar UBEC na Kasa a Sashen Hada Hannu Tsakanin hulda Gwamnati da Bangarori Masu zaman kansu (PPP).

Girma 

Abin sha’awa ne a wancan lokacin, domin duk mun san kanmu. Mahaifina soja ne kuma ya shiga aikin soja ne a lokacin Yakin Basasa, don haka ina zaune ne da mahaifiyata daga bisani kuma na koma ga kakata. A wancan lokaci ana daukar mutane ne a sanya su a makaranta, don haka ni ma na yi sa’a an dauke ni an sanya ni. Ranar da na fara zuwa makaranta sai da kakata ta fashe da kuka ni ma kuma sai da na yi kuka, a lokacin makarantar tana Bosso ne kuma da yake a wancan lokacin babu ababen hawa sosai a kafa muke takawa.

Yarinta

Abin da na fi kewa a yarintata ita ce makarantarmu ta WTC, domin kuwa tun a ranar da na fara zuwa ne aka dora mini dawainiyar kula da ’yan ajinmu. Daga karshe ma sai na zama Shugabar Dalibai ta Makarantar. Wannan abu ne na musamman

Abin da nake burun zama a lokacin da ina yarinya

Ni dama can ina son in zama Malamar Makaranta ce tun farko, ko a aji ina kiran kaina Dokta Habiba ce. Ina burin zama malamar jami’a ce, wannan shi ne burina tun ina karama. Don haka ko a Lahira in akwai aikin koyarwa shi zan yi. Ina son koyarwa, kuma ba na jin akwai wani aiki da zai yi daidai da ni in ba koyarwar ba.

Kalubale

An same su da yawa a cikin wuraren da na yi aiki za ka ga dalibai suna zuwa makaranta babu takalma a kafarsu kuma ka san makarantu ne na birni. Don haka nakan samu lokaci in je gida-gida ina wayar da kan iyayensu. Kai akwai lokacin da ma sai da na samu Dagacin Jabi na yi masa magana a kan muhimmancin iilmi, hakan kuma ya taimaka wajen karuwar yaransu da suke sanyawa a makaranta.

Lokacin kuma da na zama Shugabar Sashe wato HOD, mukamin da a kansa zan iya cirewa ko dora shugabannin makarantu na fuskanci barazana da turjiya a kai-a kai.

Babban mukami

Na fara aiki ne a matsayin malamar makaranta amma ga shi yanzu ina rike da mukamin Mataimakiyar Darakta. Don haka ka ga ana samun ci gaba. Sannan ban taba daukar wani malami na musamman ba da zai rika koyar da yarana a gida, ni nake koyar da su da kaina.

Darasi a rayuwa

Tun muna yara an koyar da mu mu kasance masu buri kuma masu tarbiyya, ana ba mu kananan shuka  don mu kula da su saboda a koya mana yadda za mu iya kulawa da kanmu da kuma wadansunmu. Idan zan tsaya fadin abubuwan da na koya a rayuwa sai gari ya waye ban gama ba. Amma na zauna da mutane iri-iri nagari da na banza.

Iyali

Ina da ’ya’ya biyar, kuma ganin sun girma cikin tarbiyya abin yana sanyaya mini rai. Autana yanzu yana shekararsa ta biyu a jami’a, don haka ina mai farin ciki.

Yadda na hadu da mijina

Allah Shi ne Mai abin mamaki, saboda Shi ne Yake shirya maka abin da ya dace da kai. Mijina yana aji 5 a wata makarantar firamare ne daban kafin a maido shi makarantarmu inda abokinsa yake. Kuma sai ya maido da kansa aji 2 wato ajinmu. Don haka muna a aji daya ne tun daga makarantar firamare. Amma babu wani abu da ya taba shiga tsakaninmu saboda a wancan lokacin suna dukana tunda yake na iya darasin lissafi sosai. Kuma idan malami ya yi tambaya a aji duk wanda ya ba da amsa zai sanya shi ya yi wa sauran dalibai da suka kasa amsawa duka. Don haka da zarar an tashi daga makaranta sai su tare ni su rama. Daga baya muka sake haduwa bayan mun gama firamare a lokacin ina jiran in samu shiga Kwalejin Kueens College ta Legas, sauran zance kuma tarihi ne.

Abin nake so game da shi

Shi mutum ne mai da’a sosai kuma yana kula da iyalansa da kyau.

Abubuwan da suke kan gaba  a abin da nake fata

Ina son kusanci da Ubangijina, in kasance mai godiya a gare Shi. Na biyu kuma ina son ganin ’ya’yana sun yi aure don a yanzu daya ce kadai ta yi aure don haka ina fatar ganin sauran a dakunan aurensu. Sannan ina son in ga na kai kololuwa wajen aikina, don a yanzu ni Mataimakiyar Darakta ce kuma ba na fata in ajiye aiki a wannan matsayi, fatata in kara sama da yardar Allah.

Wakar da na fi so

Wakokin Reggae irin na Bob Marley

Manhajar sadarwa da nake fara dubawa idan na farka da safe

Ita ce ta Facebook

Kayan kwalliya da na fi so

Ba na zama ba tare da turare ba ko dare ko rana

Takalmin da na fi so

Saboda shekaru sun yi nisa ba na sanya takalma masu tudu sosai

Kayan da na fi son sanyawa a jiki

Senegal, saboda na Afirka ne kuma suna da nagari

Abincin na fi so

Tuwo da miyar kubewa danya wacce ba mai a ciki

Yadda nake hutu

Ina zama a kan darduma in kali  talabijin.

Shawarar da mahaifiyata ta taba ba ni wacce ba zan manta da ita ba

Takan ce da ni ‘ki kasance mai gaskiya kuma ki fadi abu a yadda yake.’

Shawarata ga matasa

Su yarda da kansu kuma su jajirce kwarai kada su zamo masu cika buri kuma kada su kasance masu son tara abin duniya sosai. Su kuma jira lokacinsu ba gaggawa a rayuwa. Iyali

Su yarda da kansu kuma su jajirce kwarai kada su zamo masu cika buri kuma kada su kasance masu son tara abin duniya sosai. Su kuma jira lokacinsu ba gaggawa a rayuwa.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos