Yadda almajiri ya rasa hannayensa saboda zargin satar wayar salula
Wani yaro almajiri dan shekaru 13 a duniya mai suna Zubairu Yusha’u ya rasa hannayensa biyu sakamakon azabar da malaminsa na makarantar tsangaya da ke Gombe ya yi masa kan zargin satar wayar salula. Zubairu wanda shi ne na biyu a gidansu, an haife shi ne a kauyen Lakkau da ke cikin karamar […]
Wani yaro almajiri dan shekaru 13 a duniya mai suna Zubairu Yusha’u ya rasa hannayensa biyu sakamakon azabar da malaminsa na makarantar tsangaya da ke Gombe ya yi masa kan zargin satar wayar salula.
Zubairu wanda shi ne na biyu a gidansu, an haife shi ne a kauyen Lakkau da ke cikin karamar hukumar Yamaltu Deba da ke jihar Gombe.
Rahotanni sun nuna cewa yaron ya bar gidansu ne shekaru uku da suka gabata tare da dan’uwansa mai shekaru bakwai bayan rasuwar mahaifiyarsu yayin haihuwa.
An sanya Zubairu da yayansa a makarantar tsangaya da ke da almajirai dubu daya da 500 a unguwar Kagarawal da ke wajen garin Gombe.