Yadda al’ummar Esuk Mba a Kuros Ribas suke ci gaba da cinikin furfure har yanzu
Duk da ce an samu wayewa ta zamani da kuma kudin da kasa ke amfani da su, shekara 59 da samun mulkin kan Najeriya, har yanzu wadansu al’ummomin sassan kasar nan na gudanar da ciniki furfure ko ba-ni-gishiri-in-ba-ka-manda. Jihar Kuros Ribas mai cike da al’adu da iri-iri da halayar mutane daban-daban har yanzu akwai wata […]
Duk da ce an samu wayewa ta zamani da kuma kudin da kasa ke amfani da su, shekara 59 da samun mulkin kan Najeriya, har yanzu wadansu al’ummomin sassan kasar nan na gudanar da ciniki furfure ko ba-ni-gishiri-in-ba-ka-manda. Jihar Kuros Ribas mai cike da al’adu da iri-iri da halayar mutane daban-daban har yanzu akwai wata kasuwa da ke Karamar Hukumar Akpabuyo da ake kasuwanci ta hanyar cinikin furfure ko ba-ni-gishiri-in-ba-ka-manda. Duk da a shekarun baya mun bayar da irin wannan labari, ganin cewa yanzu ana mulki na dimokaradiyya ne mutane da dama sun dauka wannan lamari zai sauya amma sai gashi har yau ana wannan salon ciniki a wannan kasuwa.
A Jihar Kuros Ribas dai an taba samun wadansu mutane da suke bayar da ’ya’yansu mata jingina su karbi kayan abinci.
A wannan karo Aminiya ta leka kasuwar Esuk Mba da ke Karamar Hukumar Akpabuyo inda mutane ke ci gaba da kasuwancin furfure ko ba-ni-gishiri-in-ba-ka-manda a kasuwar da ke ci duk ranar Asabar a wani kayyadajjen lokaci wato awa biyar daga karfe 7:00 na safe zuwa karfe 12:00 na rana.
Kayayyakin da ake kaiwa kasuwar don sayarwa sun kunshi doya da gishiri da garin kwaki da garin fulawa da magi da danye da busasshen kifi da kaji da nama. Sauran su ne manja da man girki da tumatur da tattasai da sabulan wanka da wanki.
Wakilimu ya gano cewa yadda ake cin kasuwar shi ne mabukacin manja zai je kasuwar da doyarsa kwaya hudu ya nemi mai sayar da manja, sai ya ba shi doyar shi kuma ya karbi galan din manjan. Ga wanda yake son sabulun wanka ko na wanki shi kuma magi yake bayarwa sai a ba shi sabulan. Kuma wanda yake son a ba shi kifi shi kuma kaza yake bayarwa ya danganta da yawa da kuma kimar kazar da ya je da ita.
Aminiya ta gano cewa kudi dai ba su da wani tasiri a kasuwar domin idan mutum ya je da kudinsa a hannu haka zai dawo da su koda kuwa abinci mutum zai ci sai ya nemi masu ganyen miya ya ba su gari su kuma su ba shi nau’in abincin da yake bukata.
Wannan kasuwa ta samo asali ne tun 1956 wato shekara 63 da suka gabata, lokacin da Turawa suke yi wa Najeriya mulkin mallaka. Kasuwar wata cibiya ce ta saye da sayar da bayi ana ketarawa da su zuwa Nahiyar Turai a wancan lokaci.
Shugabar Kasuwar, Ekaette Asukuo ta shaida wa wakilinmu cewa, wannan kasuwa “Mun gaje ta iyaye da kakanni tun lokacin da Turawa suka zo yankin nan suka yi mulkin mallaka suka tafi suka bar mana gadonta. Ka ga irin sauran ginin da suka yi, suka tafi suka bar mana. Tun daga 1956 da suka kafa kasuwar suka tafi muka gaji wurin daga iyayenmu haka ake ta yin wannan kasuwanci furfure.”
Haka kuma wakilinmu ya ziyarci Layin Etim Edem da ke Karamar Hukumar Kalaba ta Kudu da ake dakon kayan masarufi ana tafiya cin waccan kasuwa inda ake kai buhunan shinkafa da katan-katan na sabulan wanka da wanki da magi da man girki da sauransu zuwa kasuwar.
Misis Emem Enoh wata ’yar kasuwa da ta saba cin waccan kasuwa ta ce, “Ko da wasa ba zan taba barin cin waccan kasuwa ya wuce ni ba. Idan ban ci waccan kasuwa ba, na bar ciniki da samun kudi ya wuce ni ke nan, don haka babu makon da ba na zuwa cin kasuwar.”
Wakilinmu ya ga dimbin mutanen karkara da kauyuka suna kwarara zuwa kasuwar kuma kowa ba kudi yake rikowa ba face nau’in abin da yake so ya bayar musaya a ba shi wanda yake so.