Yadda al’ummar kauyen Daga suka ja daga da ’yan fashi
A ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe 2 zuwa 3 na dare mutanen kauyen Daga da ke karamar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina suka samu kansu a cikin rudu da jimami bayan da wadansu ’yan fashi da makami suka rika bin su gida-gida suna kwace musu kudi. Malam Haruna Bello daya daga cikin […]

A ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe 2 zuwa 3 na dare mutanen kauyen Daga da ke karamar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina suka samu kansu a cikin rudu da jimami bayan da wadansu ’yan fashi da makami suka rika bin su gida-gida suna kwace musu kudi.
Malam Haruna Bello daya daga cikin wadanda suka kai dauki kuma suka yi artabu da ’yan fashin ya shaida wa Aminiya cewa ’yan fashin sun fara kai hari ne a gidan wani mai suna Alhaji Salmanu amma ba su same ba, saboda ya kaurace wa kwana a gidan sakamakon biyo shi da wadansu varayin suka yi a kwanakin baya daga kasuwar Kagadama.
“To da suka shiga gidan sun bukaci matarsa ta ba su kudi ko ta nuna musu inda mijin yake ajiye kudinsa amma ta ce ba ta sani ba kuma ba ta san inda mijinta ya tafi ba. Sun samu Naira dubu biyu a wajen ta. Da suka fito daga gidan sai suka shiga gidan Malan, dauke da makamai ciki har da bindiga kirar AK 47, inda suka kwace Naira dubu 20 daga wajensa, sannan suka tasa keyarsa suke ce ya kai su gidan Alhaji Buhari. A lokacin da suka je kofar gidan Alhaji Buhari ne, sai Malan ya nuna masu gidan wani dattijo mai suna Alhaji Buzu, sai daya daga cikinsu ya leka ya ga Alhaji Buzu a zaune yana lazimi, ya juyo kan Malan ya ce, wannan ba shi ne Alhaji Buhari ba.” inji shi.
Ya ce nan suka tilasta masa ya nuna gidan, kuma bayan ya nuna musu gidan sai suka sake shi suka ce ya gudu su kuma suka shiga cikin gidan dama kofar ba a rufe take ba, saboda yanayin zaman kauye. “To sai Malan ya shiga yin kururuwa yana neman gudunmawar jama’a, bayan sun sake shi, sai gari ya dauki harami, matasa da dattawanmu duk wanda ya ji aka yi ta fitowa ana nufar kofar gidan Alhaji Buhari inda ake jin kururuwar. Ashe da suka shiga gidan, sun kawo Alhajin zauren kofar gida sun rufe kofar, sai wadansu suka tsallaka ta katanga suka shiga.To jin hayaniya ta yi yawa, sai muka ji dayansu yana cewa, ‘ka harbe su,’ daya kuma na cewa, ta ki tashi. Sai aka ce a hau sama a huda rufin, bayan an samo diga wadansu suka hau aka bude rufin sai aka kawo kara da ciyawa aka rika jefawa ciki aka bi da ashana aka kunna wuta har da shi Alhajin a ciki. Da farko suka rika kashe wutar da aka zuba fetur aka sake kunna wutar ba a dauki lokaci ba sai suka bude kofar suka jefo Alhajin da nufin dauke hankalin jama’a. Har an fara sanya masa sanda bisa zaton dayansu ne, sai aka gane shi ne,” inji Malam Haruna.
Ya ce, a karshe su da kansu varayin suka rika fitowa daya bayan daya ana buge su har su mutu.
Aminiya ta samu labarin cewa ,bayan an kashe varayin wadansu daga cikin mutanen da suka kai daukin sun gane fuskoki da sunayen biyu daga cikin varayin uku, masu suna Abdussalam da Adamu da suke zaune a wasu ’yan bukkokin da suka yi a cikin dajin hanyar zuwa kauyen Ginzo.
Da Aminiya ta tuntuvi Mai unguwar kauyen Magaji Daga, Alhaji Sa’idu Mamman ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce, a kofar gidansa aka kawo gawarwakin kafin isowar jami’an tsaro saboda babu su a kusa.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina DSP Isa Gambo ya tabbatar faruwar lamarin.