Yadda Amarya da ango suka mutu ranar da aka daura musu aure a jirgi

Wata amarya da angonta a Jihar Tedas ta Amurka sun mutu sakamakon hatsarin da jirgi mai saukar ungulu samfurin Bell 206B da ke dauke da su ya yi lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga wurin liyafar aurensu, in ji wasu jami’ai. Will Byler da Bailee Ackerman Byler dukkansu dalibai ne a Jami’ar […]

Yadda Amarya da ango suka mutu ranar da aka daura musu aure a jirgi

Yadda Amarya da ango suka

Wata amarya da angonta a Jihar Tedas ta Amurka sun mutu sakamakon hatsarin da jirgi mai saukar ungulu samfurin Bell 206B da ke dauke da su ya yi lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga wurin liyafar aurensu, in ji wasu jami’ai.

Will Byler da Bailee Ackerman Byler dukkansu dalibai ne a Jami’ar Sam Houston. Wata jaridar dalibai ce ta soma ba da rahoton hatsarin nasu.

Ma’auratan sun yi hatsarin ne a kusa da Ubalde, kimanin mil 85 da yammacin San Antonio.

A cewar rahoton BBC Hausa, Mutanen da suka halarci liyafar tasu sun yi ta mika ta’aziyyarsu a sakonninsu da suka wallafa a shafukan zumunta.

“Na yi matukar kaduwa!” In ji wani abokin ango a sakon da ya wallafa a Facebook, yana mai karawa da cewa matukin jirgin ma na cikin wadanda suka mutu.

A wata sanarwa da shugaban daliban jami’ar ya fitar, ya ce za a rika tunawa da ma’auratan saboda kirkinsu.

Ma’auratan sun yi hatsarin ne sa’a biyu bayan an daura musu aure.

Jaridar da ake wallafawa a jami’ar ta ruwaito cewa Will Byler na karantar aikin gona kafin mutuwarsu.

Tabbas ’yan Najeriya na cikin matsin rayuwa — Kalu

Ambaliya: Binani ta bai wa Maiduguri tallafin 50m

An sallami sojar da ta zargi shugabanta da neman lalata da ita

CBN ya ƙara kason kuɗin ruwa zuwa 27.25 cikin 100