Yadda ambaliya ta yi fata-fata da birnin Houston
Matsanan ciyar guguwar Harbey ta kai farmaki a Kudu maso Gabashin Jihar Tedas ta Amurka, inda a ranar 25 ga Agusta ta yi fata-fata da birnin Houston , inda mutane suka jigata, har aka yi asarar rayuka tara daidai lokacin da masu fafitikar ceton rai ke ta kokari ruwa ya kawo mutane kugu. Jami’an Hukumar […]

Matsanan ciyar guguwar Harbey ta kai farmaki a Kudu maso Gabashin Jihar Tedas ta Amurka, inda a ranar 25 ga Agusta ta yi fata-fata da birnin Houston , inda mutane suka jigata, har aka yi asarar rayuka tara daidai lokacin da masu fafitikar ceton rai ke ta kokari ruwa ya kawo mutane kugu.
Jami’an Hukumar Jihar Tedas sun tabbatar da mutuwar mutum tara a sanadiyyar wannan guguwa da aka yi wa lakabi da Hurricane Harbey. Wadanda suka mutu sun hada da mutum shida a garin Harris County da ke birnin Houston; da wnai mutum a Rockport da ke kusa da inda guguwar Harbey ta taso, sai kuma wani mutumin da ya rasa ransa a garin La Markue kusa da galbeson.
Hukumomin suna sa ran karuwar adadin wadanda suka rasa ransa, daidai lokacin da ake kokarin aikin ceton rai, ga kuma ruwan sama mai karfi da ya tumbatsa koguna, har suka yi ambaliya a gabar teku. Masu has ashen yanayi sun ce akwai yiwuwar a samu karin ruwan sama da inci 20 da zai baibaye Jihar Tedas da Louisiana zuwa Alhamis din wannan makon.
Kimanin mutum dubu biyu aka ceto, kuma har yanzu suna matukar bukatar taimako. Duk da kokarin da ake yi an danganta mace-macen da guguwar Harbey, wadda ta haifar da dimbin asarar dukiya, kuma tana ci gaba da kadawa a birnin Houston da daukacin tedas da Louisiana. Jami’an hukuma sun yi gargadin cewa ambaliyar za ta ci gaba, inda suka yi nuni dacewa fiye da mutum dubu 30 zai zame musu dole su fice daga gidajensu.
“Har yanzu ba mu fita daga matsala ba,” a cewar Elaine Duke mai rikon Sakataren tsaron Homeland Security kamar yadda yake kunshe a bayanin da ya gabatar a birnin Washington . “Har yanzu guguwar Harbey ta kasance mafi munin hadari a tarihi,” inji shi.