Yadda ambaliyar ruwa ta durkusar da kasuwanci a Kantin Kwari
‘Yan kasuwar sun dora alhakin ambaliyar akan gwamnati a bisa gine-ginen da ta yi a cikin kasuwar.
Mamakon ruwan sama da aka yi na ‘yan kwanaki a Kano ya haifar da ambaliya a kasuwar Kantin Kwari wadda ta janyo asara ta miliyoyin naira.
Ruwan saman da aka yi shi kamar da bakin kwaira na ranar Litinin ne ya dada tayarwa da ‘yan kasuwar hankali yayin da ya yi ambaliyar ta cika kwatoci da magudanan ruwa, ta kuma kwarara har cikin shagunan jama’a.
Da yawa daga cikin ‘yan kasuwar na dora alhakin ambaliyar akan gwamnati a bisa gine-ginen da ta yi cikin kasuwar da kuma manyan layukan da sayar da su, wanda suka toshe magudanan ruwa.
Bugu da kari, ginin gadar sama da gwamnatin ke yi, ta yi shi ne kan babbar magudanunar ruwa, da ruwansu ke fitowa daga unguwannin Gyadi-gyadi da Sabon titi da Mandawari ya bi ta Fagge.
Sai dai gwamnatin tana dora alhakin ambaliyar kacokam kan dan kwangilar da ke aikin hanyar gadar saman.
Ga dai hotunan wasu wuraren da ambaliyar ta ci.