Yadda Aminu Kano ya tallafa da sule 10 don kubutar da Sardauna daga shari’a

Me ya sa Sardauna da Zik da Awolowo suke da alaka mai kyau duk da adawar siyasa? Sardauna da Azikiwe sun dade da sanin juna ban sani ba. Wata rana mun je Kaduna sai Zik ya je wurin Sardauna kuma bai dawo ba sai kusan karfe 9:30 na dare. Da ya dawo sai ya aika […]

Yadda Aminu Kano ya tallafa da sule 10 don kubutar da Sardauna daga shari’a

Me ya sa Sardauna da Zik da Awolowo suke da alaka mai kyau duk da adawar siyasa?

Sardauna da Azikiwe sun dade da sanin juna ban sani ba. Wata rana mun je Kaduna sai Zik ya je wurin Sardauna kuma bai dawo ba sai kusan karfe 9:30 na dare. Da ya dawo sai ya aika aka kira ni, na iske yana zaune a kan tebur da gorar fura. Sai ya ce in kawo kofin gilashi, na kawo ya zuba min fura rabin kofi, sai na ce mu ba a zuba wa mutum fura kadan. Sai ya ce zan sha ko ba zan sha ba. Na ce ina ya samu fura? Ya ce wajen Sardauna. Na ce yaya ka san Sardauna? Sai ya yi dariya, ya ce rigimarsa da ni yawan tambaya, in sha fura mana kawai. Na ce sai an yi min bayani don Malam Aminu Kano ya koya min in ban san abu ba in yi tambaya don a yi min bayani saboda wata rana za a tamabaye ni, kada in ka sa bayani. Sai ya ce Sardauna ya yi aikin dan jarida mai zaman kansa na mujallar Zik mai suna “West African Pilot,” in ya aiko min da labari, sai in aika masa da kudinsa. Sannan suna da alaka da Awolowo sai dai sun fi sabawa da Zik tun kafin su fara takara.  

Me ya sa Sardauna da Aminu Kano suke zumunci ba kamar yadda ake siyasa yanzu ba?

Sardauna yana Hakimin Gusau sai aka yi zargin ya ci kudin En’e, amma ainihin rigimar shi ne sun nemi sarauta da Sa Abubakar don neman zama Sarkin Musulmi. Sai Sardauna ya ce ta yaya Sa Abubakar dan mace zai zama Sarki. Amma kawunsu Sarkin Musulmi Hassan ya bar wasiyya ga dansa Lamido cewa kada ya nemi sarauta, ya bar wa Magatakarda Abubakar har aka nada shi Sarkin Musulmi. Wannan jikakkiyar ta sa suka ce sun daure Sardauna wata shida. Sai Sardauna ya aika wa Zik, sai ya ce zan yi kokari in sama maka lauya. Amma ka samu ’yan uwanka ’ya’yan sarauta su tara maka kudin lauya. Sai Sardauna ya ce to, sai ya gaya wa amininsa Iyan Zazzau Aminu, lokacin Ciroman Kano Muhammdu Sunusi kafin ya zama Sarkin Kano kakan Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II na yanzu da sauransu. Cikin wadanda suka tara kudin har da Malam Aminu Kano. Domin Aminu Kano ya fito daga Kano zai shiga jirgin kasa da ake yi wa lakabi da dan-Zariya da ke zirga-zirga daga Zariya zuwa Jos ya dawo ya koma sannan ya kwana. Aminu Iyan Zazzau ya je tashar jirgi sai ya ga Malam Aminu Kano da matarsa suna zaune a benci, sai ya yi sallama ya ce lafiya, sai ya ce za su shiga dan-Zariya ne zuwa Jos don yana koyarwa a Makarantar Midil ta Bauchi a matsayin Mataimakin Abubakar Tafawa balewa. Sai Iyan Zazzau ya gayyace shi masaukinsa. Da Malam Aminu Kano ya isa Bauchi sai ya rubuto wa Aminu Iya takarda yana godiya, shi kuma sai ya rubuta masa cewa suna neman alfarma don suna cikin matsala shari’ar Sardauna. Sai Malam Aminu ya rubuta cakin kudi na Sule 10 da takarda ya ce ka san daga cikin albashina abin da zan iya bayarwa ke nan. Aka yi shari’a a Zariya aka sallami Sardauna aka ce ba ya da laifi. Aminu ya ba Sardauna manyan riguna ya koma gida Sakkwato. A 1949 aka yi zabe za a kafa Majalisar Mulki ta Arewa, Saudauna ya ci zabe daga Sakkwato ya zama shugaban aikin gwamnati a 1950 a Arewa. Sai Allah Ya karbi ran Malam Ja’afaru dan Isyaku a 1957. Masu neman sarauta su ne Aliyu Turaknin Zazzau da Nuhu Bammali Magajin Garin Zazzau da kuma Aminu Iyan Zazzau. Sai Sardauna ya sa aka kira masu nada sarauta, ya ce kun san dalilin da ya sa na kira ku, suka ce a’a. Sai ya ce ina neman alfarma, suka ce na me, ya ce mutumina shi ne Aminu Iyan Zazzau. A taimaka a ba shi sarauta, suka ce kana shugbanan  Arewa ka ce kana neman abu mu ce a’a. Aka nada Aminu, bayan ya natsa, sai ya je ga Sardauna ya ce ga sunayen wadanda suka ba da gudunmawa aka biya lauya. Da Sardauna ya duba sai ya ga an ja layi a karkashin sunan Malam Aminu Kano. Sai ya ce Shugaban ’yan NEPU ya ban gudunmawa. To lokacin da Sardauna ya bar Kwalejin Katsina, Aminu Kano bai je Kwalejin Gwamnati ta Kaduna ba. Sardauna dan 1926 ne, Musa ’Yar’aduwa da Shettima Kashim ’yan 1925 ne. Aliyu Makaman Bidda da Ahmad su suka bude Kwalejin Katsina a 1921. Abubakar Tafawa balewa da Sa’adu Zungur ’yan 1928 ne. Aminu Kano dan 1937. Sardauna ya ce yanzu wannan ya ba da taimako a kaina. Wata rana Aminu Kano ya zo Kaduna ya yi lacca ya yi babatunsa, sai Sardauna ya aika aka kira masa Malam Bala Keffi, Shugaban NEPU a Kaduna lokacin yana Firimiyan Arewa. Sai ya ce ciyaman bakonka nake son in gani Aminu Kano. Sai ya ce ba komai, ya je ya gaya masa Sardauna na son ganinsa, ya ce to bismillah. Suka tafi Sardauna na zaune da ministoci, da ya ga Malam Aminu Kano yana zuwa sai ya tashi ya zo ya rungume shi suka shiga dakin karatu a gaban su Sule Gaya da Ibrahim Musa Gashash da sauransu suna mamaki. Sardauna ya kulle kofa ya ce na kira ka ne in gode maka alherin da ka yi min. Sai Aminu Kano ya ce in ba mu taimaka wa juna ba, me za mu yi, ni na manta ma. Sardauna ya ce in ka manta, ai ni da ka yi min alherin ban manta ba. Don Allah in ka kare lacca ka dawo, don ka san ba zan iya kiranka a Kano ba don zafin siyasa.  

Ka san Ibo, mene ne halin Ibo da Yarbawa da Hausawa da sauran ’yan Najeriya?

Manyan da daban suke, Ibon da ya fara zuwa Wamba mahaiifina ya fara ba shi filin ya gina gida. Ni na tashi a dan Najeriya ban san kabilanci ba. Su Ibo sun tashi ba su da gari, garuruwan Umu’ahiya da Aba da kuma Enugu ba su suka kafa su ba, garuruwan Turawa ne wato bariki ne da suka kafu saboda titin jirgi, wato garuruwan Gwamna ne kamar yadda Turawa suka kafa Kaduna. Ibo sun tashi a gidaje da zuriya suke kafawa “Clan.” Shi ya sa suke cewa su suna zaune a yanki mai cin-gashin kansa “autonomous.” Wato suna ganin su zaman kansu suke, don haka Ibo bai san akwai wani Ibo a mil 20 daga inda yake ba. Ya kamata ’yan Najeriya sun san cewa an zauna kusan shekara 100 tare, an haifi NnamdiAzikiwe a Zungeru a Arewa, an haife wani mai daukar hoto mai suna Papa Ogbabu a Jos a 1930, Ibo ne dan asalin Owerri. Zik ya sa su rika taro duk ranar Lahadi har wancan ya ce ya ga zuriyarsu kusa da kauye kaza, shi ma wancan ya fadi sannan ga inda ya fito. To yaya za ka hada sauran ’yan Najeriya da wanda ba ya da gari. Ku kuma ’yan Najeriya kuna da al’ada da tsarin mulki kafin zuwan Turawa. Ibo shi mai neman abinci da arziki ne don shi ke sayar da gas da kananzir da sauransu. Allah Ya ce ku yi adalci don haka don me za ka hana su neman abinci, kada mu kore su. Idan akwai Bahaushe da Bayarabe da Ibo a ofishi daya kuma akwai wurin ajiye mota biyu, idan Ibo ya fara zuwa aiki, zai gicciye motarsa ce a wurin da za a iya ajiye motoci biyu domin shi ya taso bai san ya raba wuri da wani ba, shi kansa kawai ya sani.   

Yaya aka yi dan Arewa daga Sakkwato Alhaji Umaru Altine ya zama Magajin Garin Enugu?

Zik Najeriya ce mazabarsa ba kasar Ibo ba, ya tsayar da Malam Umaru Altine aka zabe shi Magajin Garin Enugu haka kuma da ya yi tazarce, aka kara zabensa a karo na biyu.  

Mene ne alakarka da Dokta Aled Ekwueme?

Ni na kawo Dokta Aled Ekwueme na hada shi da Alhaji Shehu Shagari har ya ba shi mutsayin Mataimakin dan takarar Shugaban kasa a 1979, kuma suka ci zabe.  

Jama’a sun amfana da samun mulkin kai kuwa?

An amfana, don muna da kasa mun fita daga bauta, muna mulkin kanmu kuma mun yi kura-kurai.   

Wadanne manyan matsaloli muka samu?

Matsalarmu ita ce da sojoji suka shiga lamarin siyasa. Eh manyanmu suna son kasar amma sukan yi surutai da suka shigo sai kabilar Ibo wadda ba su san ma’anar kasa ba balle su gina ta. ’Yan kabilar Ibo suna ganin za su iya kwace kasar karfi-da-yaji suna ganin in sun kashe manyanmu ba za a ce wani abu ba, domin su samu kasar. Shi ne kuskuren da suka yi.   

Kai dan siyasa ne kuma dan kasuwa, ko kana da alaka da sojoji?

Ai a babban gida na tashi, kowa nawa ne. Na san sojoji da yawa, don aka yi juyin mulkin Murtala ran 29 ga Yulin 1975, sai Janar Joe Garba ya yi sanarwa, bayan nan sai ya kira ni domin ba su yanke waya ba kamar yadda aka saba. Ya ce in zo suna son su gan ni, sai na ce kuna sanarwar juyin mulki ku ce kuna son ku gan ni? Sai ya ce ba komai, sai na je barikin Dodan Barrack na iske mutum biyar, Joe Garba da Paul Tarfa da Babangida da Shehu ’Yar’aduwa da Abdullahi Muhammad. Sai Tarfa ya ja ni gefe ya ce suna son in je in gaya wa Birgediya Ikwue wanda Idoma ne kuma dan Arewa mai kula da sojan sama da Janar Ejoor shugaban sojan kasa da Admiral Soror shugaban sojan ruwa. Na tuka mota na je Lamba 57, Aledander na ce da matarsa Baturiya ina Ikwue sai ta ce yana gidan Soror suna taro, sai na ce ta gaya masa ana son ganinsa, ta ce za ku kashe mana miji. Sai na ce za a kashe miki miji ne za a turo ni. Ta gaya masa ya je ya same su, sai Shehu ’Yar’aduwa ya ce za mu yi sauyi don akwai abubuwa da yawa da an so a janyo hankalin Janar Gowon amma bai damu ba. Za su yi wa Ejoor da Admiral Soror ritaya, amma shi za su ci gaba da aiki da shi, sai ya ce da Kanar ’Yar’aduwa sai dai ku hada da ni, yaya za ku yi ritayar mutanen Kudu ko bar ni, ai irin wannan ne kuskuren da Ibo suka yi suka janyo rigima. Aka tura Kanar Wushihi da Kanar Duba Kano su dauko Murtala don sun je Polo da Birgediya Mobolaji Johnson Gwamnan Legas da Birgediya Wale Rotimi. Ya ce Murtala zai zama Shugaban kasa.  

Wace shawara za ka bayar don ganin Najeriya ta samu daukaka?

Matsalar ita ce ’yan siyasa na kwarai sun ja gefe saboda ’yan cuwa-cuwa sun bata kasar. Ba mu da tsayayyun ’yan siyasa masu son gina kasa, sai dai muna da ’yan siyasa ’yan a ci ba don an yi shuka ba, wannan ce matsalar. Ka taba jin kasa ta shekara kusan dari a ce har yanzu mutanenta ba su yarda su zauna ba, ai kasar ba gaskiya.   

Mene ne ra’ayinka kan kiran da ake yi na sake fasalin kasar nan?

Tun muna Kudu da Arewa aka koma jihohi 12 aka koma yanzu muna da jihohi 36, to me ya rage. Ni Isyaku Ibrahim da marigayi Alhaji Garba Leko da marigayi Isyaku Jikan Malam da Alhaji Mudi a garin Sabo Ibadan mun tafi wajen Cif Adelabu mu gaishe shi amma sai Cif Richard Akinjide ya ce yano son ya bi mu. Muka je da shi muka gabatar da shi domin Cif Adelabu bai san shi ba. Sai Adelabu ya kira Garba Leko da Isyaku Jikan Malam ya ce shi fa ba ya son lauyoyi a cikin jam’iyyarsa saboda rigimarsu, amma tunda mun kawo shi, ba komai. Aka yi zabe zuwa Ibadan Town Council a 1958 sai Adelabu ya sa aka kira mu ya ce wannan lauyan da kuka kawo ku kira shi, shi ne muka kira Richard Akinjide ya tsayar da shi ya ci zabe a Ibadan. A 1959 aka zo zaben majalisar kasa, ni na yi masa kamfe a Sabo-Ibadanm da Mokwalla da Jami’ar Ibadan, muka ci zabe. Daga nan Sa Abubakar Tafawa Balewa saboda hadin gwiwa ya ba shi Ministan Ilimi. A 1979 da muka cin zabe Shagari ya kuma ba shi Ministan Shari’a kuma duk taron tsarin mulkin kasar nan da shi aka yi, amma wai yana fadin a sake fasalta kasa. Irin wadannan ba dattawa ba ne, ba sa son Najeriya illa kansu. Duk ranar da dan siyasa ya ce yana son kansa fiye da kasa, to za a dade ana samun rigima. Farfesa Wole Soyinka da sauransu suna cewa a sake tsara kasa, to wane bango ya fashe balle a sake fasaltawa? Har da ’yan Arewa suke surutu ba tare da sun yi tambaya ba.

Da ka fita waje dan Najeriya ake ce maka ba dan bangare Hausawa ko Ibo ko Yarbawa ba. Wadansu suna munakisa suna tsoron za su fadi a zabe sai suke neman a sake salo. Ina rokon Allah a samu zaman lafiya.  

Yaya aka yi ka shiga harkar siyasar Afirka da ta duniya?

Ina da abokai da dama don na yi karatu a Rasha da Jamus, na kafa kamfani inda Shugaban Ghana na yanzu Mista Nana Akufo-Addo ya yi aiki a kamfanina a Faransa, ni na kafa kungiyar manyan ’yan kasuwan Afirka (African Business Roundtable) wadda Bamanga Tukur ke jagoranta a yanzu. Na yi wa jama’a kamfe sun ci zabe a Amurka kamar Bill Clinton da sauran mukamai da dama. Ya kamata mu rika darajta mutun don a gina Najeriya da Afirka baki daya.