Yadda Arsenal za ta iya lashe Firimiyar Ingila
Sai dai har yanzu Firimiyar Ingila akwai sauran rina a kaba tsakanin Manchester City da Arsenal.
Ranar Lahadi mai zuwa ce za ta kasance ranar karshe da za a rufe wasu daga cikin gasannin nahiyar Turai da wasu sassan duniya.
Tuni a wasu gasannin aka samu wadanda suka lashe su, kamar Bundesliga da La Liga da Serie A.
- Kashi 28.5 na Kanawa na fama da hawan jini — Kwamishinan Lafiya
- An ƙaddamar da gidan rediyon EFCC mai yaƙi da labaran ƙarya
Sai dai har yanzu Firimiyar Ingila akwai sauran rina a kaba, domin kuwa wasan da ya rage shi ne zai bayyana gwarzon gasar tsakanin kociyan Manchester City, Pep Guardiola da takwaransa na Arsenal, Mikel Arteta.
A yanzu haka teburin gasar ya nuna Manchester City ce ke jagorantar Firimiyar da maki 88 tazarar maki biyu tsakaninta da Arsenal.
Ita kuwa Arsenal da ke mataki na biyu da maki 86, ta zarce Manchester City da kwallo guda, inda take da 61 ita kuma City na da 60.
A wasan na ranar Lahadi, Manchester City ta kece raini da West Ham, yayin da Arsenal za ta barje gumi da Everton.
Wacce dama ko wacce kungiya ke da ita ta lashe wannan gasar?
BBC ya yi fashin baki dalla-dalla kan ko wanne yanayi da za a iya tsintar kai a ranar Lahadi ga masu ruwa da tsaki a fagen tamaula.
Idan Arsenal ta ci wasanta ita ma City ta ci nata, City ta zama zakara kenan da tazarar maki biyu.
Idan aka yi janjaras da City da West Ham da za su yi fafatarwar karshe, Arsenal ta ci to maki ya zo ɗaya amma kwallaye ne za su raba gardama.
Idan aka ci City ita kuma Arsenal ta ci nata wasan to Arsenal ta zama gwarzuwar gasar Firimiyar 2023/2024.
Idan kuwa aka ci Arsenal, City ta ci Firimiya. Kazalika, City za ta iya lashe idan Arsenal ta yi canjaras.
A don haka yanayi guda Arsenal ke fatan gani a ranar Lahadi, a ci Manchester City ita kuma ta ci.
Sai dai wani abu mai kamar wuya inji masu iya magana amma Hausawa na cewa ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare. (BBC)