Yadda Bahaushe yake sarrafa harshe wajen isar da sako

A wannan makon, shafin Adabi zai waiwayi yadda Bahaushe ke sarrafa harshe wajen isar da wani sako cikin hikima. Akwai hanyoyi da dama da ake amfani da su wajen isar da sakon. Ga wasu daga cikin salon magana a kasar Hausa.  Karin Magana  Gabatarwa Karin magana salo ne na yin magana takaitacciya kuma dunkulalliya wacce […]

Yadda Bahaushe yake sarrafa harshe wajen isar da sako

A wannan makon, shafin Adabi zai waiwayi yadda Bahaushe ke sarrafa harshe wajen isar da wani sako cikin hikima. Akwai hanyoyi da dama da ake amfani da su wajen isar da sakon. Ga wasu daga cikin salon magana a kasar Hausa.

 Karin Magana

 Gabatarwa

Karin magana salo ne na yin magana takaitacciya kuma dunkulalliya wacce ke dauke da ma’ana mai fadi don isar da sako ta cikin hikima. Akan yi amfani da wannan salo wajen yin nuni, gargadi, yabo, karfafa gwiwa, da sauransu duk a hikimance, ta yadda kusan in ba cikakken Bahaushe ba, fahimar wannan zance yana da wahala.

Ma’anar Karin Magana

Masana Harshen Hausa sun fassara karin magana gwargwadon fahimtarsu. Daga ciki akwai:

Farfesa Dangambo da ya ce, “Karin magana dabara ce ta dunkule magana mai yawa a cikin zance ko ’yan kalmomi kadan, cikin hikima.”

Yahaya, Zariya, Gusau, da ’Yar’aduwa kuwa cewa suka yi, “Karin magana tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajarce na hikima da zalaka tare da bayar da ma’ana gamsasshiya, mai fadi, mai yalwa, musamman idan aka tsaya aka yi bayani daki-daki.”

Ke nan idan aka lura sosai, za a ga cewa ita karin magana, magana ce dunkulalliya wacce ba kowa ne zai iya gane ta ba tare da an yi masa cikakken bayani ba. Amma yau da gobe da yawan amfani da ita, musamman a zamunan da suka shude, da ake yawan tsarma ta a cikin zance, sai ya zama shi Bahaushe yana iya gane abinsa. Misali, ana iya yi wa mutumin da ba ya da tattali nuni cikin ’yan kalmomi marasa yawa, kamar a ce da shi, wannan abin da kake yi zai hana ka farcen susa. Ko kuma idan ana son yin magana game da wani abu mai amfani da marar amfani. Kamar a ce idan an aikata abin, wani abu mara dadi zai faru da wanda ya aikata, to ana iya yi masa nuni ta hanyar cewa da shi, wannan abin ba zai haifar maka da da, mai ido ba da sauransu.

Kowace daya aka dauka daga cikin wadannan karin magana guda biyu, za a tarar cewa maganganu ne dunkulallu, wadanda idan aka tashi farfasa su, za su ci guri mai yawa. Amma idan aka fade su da baki ko aka rubuta su, za a ji su ko a gan su gajeru, sannan shi wanda ake magana da shi zai iya fahimtar abin da ake nufi.

Amfanin Karin Magana

  1. Takaita doguwar magana.
  2. Nuni, gargadi da fadakarwa cikin nishadi, sannan a takaice.
  3. Bayyanar da kwarewa da fasahar Bahaushe wajen iya magana.
  4. Adon harshe. Abin da ake nufi da adon harshe a nan, shi ne cewa karin magana yana kara wa zance kyau da kuma dadi.

Habaici

 Gabatarwa

Habaici salon magana ne da Bahaushe ke amfani da shi wajen isar da wani sako a hikimance ta cikin zance. Wannan sakon zai iya kasancewa gargadi, huce haushi, jan-kunne da sauransu. Magana ce da ake yin ta a cikin duhu; ma’ana, ba kai-tsaye ake fito da maganar ba, sai dai wanda ake yi dominsa ya san inda aka dosa. Ko kuma idan abin ya shafi wani laifi ne da mutumin ya aikata, to duk wanda ya san ya aikata laifin shi ma zai iya sanin inda aka dosa. Amma in ba haka ba, sanin inda aka dosa cikin habaici yana da wahala.

Yahaya, Zariya, Gusau, da ’Yar’aduwa sun ce, “Habaici kalmomi ne da ake amfani da su a fakaice don muzanta mutum.”

Dalilan da suke sa yin habaici suna da yawa, daga ciki akwai tsokanar fada, jan-kunne, gargadi, ramuwa, kishi, kyashi, hassada, rowa, aikata wani abin ki, da sauransu. Kowane daya daga cikin wadannan dalilai da aka zayyana da ma wasunsu, in suka faru sai a yi amfani da habaici a cusa wa wanda ake magana da shi haushi. Shi kuma Farfesa Dangambo cewa ya yi, “Habaici, wata hanya ce ta zagin mutum a fakaice.”

Hanyoyin da ake bi wajen yin habaici akwai gugar zana, karin magana, harbin iska da sauransu. Misali:

  1. Idan wani ya shiga sabgar wani a wani lokaci, yana iya bari sai daga baya ya ce, daga yau in mutum ya kara shiga sabgata, sai na turmumusa hancinsa a kasa. Ka ga wannan jan-kunne ake yi amma cikin habaici. Maimakon a ce wane daga yau in ka kara shiga sabgata zan yi maka kaza. Ko a ce, wane, daga yau hawainiyarka ta kiyayi ramata. A nan kuma an yi habaici ne mai kama da karin magana.
  2. Idan wani ya sayi wani abu kamar abin hawa haka, ana iya bayyana hassadar da ake yi masa ta cikin habaici. Misali, a ce, mu ma dai mun kusa sayen motar nan. Za a gane cewa hassada ce idan aka lura da cewa a nan mai fadin maganar maimaikon ya taya wanda ya sayi motar murna sai ya buge da cewa shi ma dai zai saya.
  3. Idan wani ya nuna son ya mallaki wani abu, za a iya cewa da shi, nan gani, nan bari. Ko kuma a ce kwalele dokin Iliya, ba ni sayar da kai, ba ni ba da aronka; da sauransu.

Akwai dangantaka tsakanin habaici da zambo, saboda zamowarsu duk zagi ne da ake yi wa mutum ba tare da kama suna ba. Sai dai shi zambo yakan fito da siffar wanda ake zagi ta yadda kowa zai iya gane shi.

 Zambo

 Gabatarwa

Zambo, salon magana ne da ake amfani da shi wajen bakanta wa mutum ta cikin hikima, ta hanyar bayyana siffofinsa sannan a danganta shi da aikin da ya aikata na muni. Wato a cikin zambo ana fito da surar mutum ne a fili, sannan a munana shi ta hanyar bayyanar da boyayyen mummunan aikin da ya aikata. Akan siffanta mutum matuka gaya, ta yadda duk wanda ya san shi, da ya ji zai gane  wanda aka nufa da wannan magana.

Yahaya, Zariya, Gusau, da ’Yar’aduwa sun ce, “Kalmomi ne na batawa da ake amfani da su don a musguna wa wani. Akan kwatanta kama ko hali ko dabi’a da wasu munanan siffofi ko halaye don a wulakanta mutum.”

Zambo zagi ne. Farfesa Dangambo ya ce “Zambo zagi ne na kai-tsaye, idan an kwatanta shi da habaici”. Yahaya, Zariya, Gusau, da ’Yar’aduwa sun ce wadansu sun dauki zambo zagi ne kuma kishiyar yabo.

Ke nan za mu fahimci cewa akwai dangantaka tsakanin zambo da habaici. Idan muka so ma muna iya cewa, wa da kane suke, bisa dogaro da jawabin Farfesa Dangambo, da ya zo a sama. Wato a bayyane da zambo da habaici duka zagi ne a ra’ayin Farfesa, sai dai shi habaici ana sakayawa, ba kowa zai gane wanda ake zagi ba. Amma a cikin zambo, duk wanda ya san wanda ake zagi, to da ya saurari zambon zai gane shi. Saboda haka shi zambo, wan habaici ne.

Ana yin zambo saboda dalilai masu yawa, daga ciki akwai:

  1. Kiyayya tsakanin mutane kan jawo a yi zambo don a rage wa wanda ake ki daraja a cikin mutane, ko a jawo jama’a su ki shi. Wannan kuma akan fake da wani aibi da mutum ya aikata komai kankantarsa, sai a kambama shi, a kururuta shi yadda abin zai yi muni sosai. Dubi wakar Mamman Shata ta Gagarabadau. In da yake cewa, “…shadidi, mazinaci….”
  2. Son fifita wani sama da wani. Kamar abin da ya shafi sarakuna, mawakansu kan yi zambo su bata ’yan uwansu don dai su mawakan su samu daukaka a wurin sarakunan, sannan su jawo wa shi dayan bakin jini a cikin jama’a. Dubi wakar Sani Aliyu Dandawo ta Turaki Aminu wan Maza, wurin da yake cewa: ‘‘’Yan Sarki sun raina mutane, ’yan Sarki sun raina mawaka, sun mai she mu ba mu san komai ba, in za su ba mu kyautar doki, wai su ramamme suka ba mu, ko wanda bai gani….”
  3. Sannan ana yin zambo da nufin gargadi ko jan-kunne, ko ankararwa da sauransu.

Hakika akwai gwanintar harshe a cikin zambo, saboda duka ne ba kama suna. Ana amfani da wannan gwaninta ta harshe a yi raga-raga da mutuncin mutum, kuma ba dama ya fito ya yi magana, saboda ba a kama suna ba. Don haka da zarar ya amsa, to ya bayyana kansa ke nan.

Mun dauko wannan rubutu ne daga shafin Katafaren Dakin Karatu Cikin Harshen Hausa na Rumbun Ilimi na yanar gizo