Yadda Bakano mai shekara 17 ya kirkiri na’urar mutum-mutumi
Ya ce burinsa a nan gaba shi ne ya zama injiyan kera na’urat
Wani matashi dan asalin jihar Kano mai shekara 17 ya kirkiro na’urar mutum-mutumi da yake sarrafa ta ta hanyar motsi da hannunsa.
Matashin, mai suna Isah Barde dai wanda bai jima da kammala karatun Sakandare ba, ya kera na’urar ce ta hanyar amfani da kwalaye da karafa.
- Tukin Babbar Mota Ba Na Matsoraci Ba Ne —Direban Tanka
- Daga karshe Buhari ya saki Dariye da Nyame daga kurkuku
Isah dai ya bayyana mana cewa yana da burin zama kwarare a fannin nazarin fasahar mutum-mutumin, duk da cewa iyayensa masu karamin karfi ne.
A zantawarsa da Aminiya, matashin ya ce tsawon shekara uku ya dauka yana hada na’urar, wacce ya bayyana a matsayin wani bangare burin rayuwarsa, duk da yanayin rashin kudin da yake ciki.
Isah dai na sarrafa na’urar ce ta hanyar motsi da hannayensa.
Ya ce, “Na hada wannan mutum-mutumin da takardu da kwalaye da tayar mota har ma da itace.
“Wasu sayowa na yi a kasuwar Jakara, wasu kuma mutane na roka suka bani, kamar na’urar busar da gashi da ta lalace, na samo ta ne na kwance ta na kwashi abubuwan da nake bukata,” inji shi.
A nasa bangaren, mahaifin yaron, Auwal Barde, ya ce yana alfahari da dan nasa, sai dai yana fama da rashin kudin da zai iya cika masa burin nasa.
“Kiwon kaji nake yi na siyar, don haka ba ni da halin daukar nauyin karatunsa, amma zan yi farin ciki idan aka samu wanda zai taimaka mana ya yi hakan,” inji mahifin Isah.
Shi ma dai wani dan uwan Isa mai suna Muhammad, ya ce, “Nan gaba ba mu san me zai kirkira ba da kasar mu za ta yi alfahari da shi, shi ya sa da na ga yana nuna alamun watsar da burinsa na ke ba shi kwarin guiwa.”
Iyayen na sa sun ce tun dan nasu yana da shekara takwas ya fara bayyana soyayarsa da kere-kere.