Yadda bankuna ke zaftare kudin ’yan Najeriya
Abokan huldar bankunan kasuwanci daba-daban a Najeriya sun koka da yawan kudaden da ake cajinsu a asusun ajiyarsu kamar yadda wani rahoton jaridar Daily Trust ya gano. Cibiyoyin hada-hadar kudaden dai sun bullo da sabbin hanyoyi da dama na zaftare kudaden masu ajiya da nufin kara kudaden shigarsu, lamarin da ya sa abokan huldar suka […]
Abokan huldar bankunan kasuwanci daba-daban a Najeriya sun koka da yawan kudaden da ake cajinsu a asusun ajiyarsu kamar yadda wani rahoton jaridar Daily Trust ya gano.
Cibiyoyin hada-hadar kudaden dai sun bullo da sabbin hanyoyi da dama na zaftare kudaden masu ajiya da nufin kara kudaden shigarsu, lamarin da ya sa abokan huldar suka nuna rashin jin dadinsu.
Yayin da wasu su ka hakura da kudaden da ake cire musu da sunan harajin kan-sarki, wasu kuwa sun ce ba za su lamunci kara zaftare musu wasu kudaden da sunan ladan amfani da katin cire kudi ba.
Ko a ’yan kwanakin nan sai da yunkurin daya daga cikin irin wadannan bankunan na yankar harajin kan-sarki na tsawon watanni uku daga abokan huldarsa ya tayar da kura, wanda hakan ya tilasta masa ya dawo musu da kudaden.
Baya ga wadannan kudaden, bankunan kuma na cajar abokan huldarsu harajin cinikayya (wato VAT) a kan kowacce irin hulda da suka yi a asusunsu.
Hakikanin abin da ake caji
Yawancin abokan huldar bankunan sun koka da cewa kudaden da ake zaftare musu sun hada da harajin tura kudi ta intanet, ladan amfani da injin cire kudi da dai sauransu, duk kuwa da cewa gwamnati ta ba da umarni cewa a rage irin wadannan harajin.
Wasu ka’aidoji da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sabunta a ranar 20 ga watan Disamban bara sun nuna cewa daga lokacin, a duk wata hada-hadar kudade ta kasa da N5,000, bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade za su caji Naira 10 ne kacal.
Kazalika, CBN din ya ce hada-hadar kudaden da ta haura N5,000 har zuwa N50,000, N25 za a caja, yayin da kuma za a caji N50 a kan wadda ta haura N50,000.
Sabon umarnin ya kuma dakatar da ladan amfani da katin cire kudi ga masu amfani da asusun ‘current account’, tun da dai da ma ana cire ladan kula da asusun.
Bugu da kari, Babban Bankin ya ce bankunan za su rika cire N50 a matsayin harajin amfani da katin cire kudi a duk bayan watanni uku, sabanin duk wata da bankunan su ke diba a baya.
Abin da bankuna ke samu
Wani bincike na kwana-kwanan nan da ya yi nazari a kan kudaden da bankuna 10 daga cikin 14 da ke a Kasuwar Hannayen Jari ta Kasa ya nuna cewa bankunan sun samu Naira biliyan 22, sabanin Naira biliyan 19 da suka samu a watanni ukun farkon shekarar da ta gabata.
Hakan dai na nuna cewa an samu karin Naira biliyan biyu da miliyan 900, wanda hakan ke nuna samun karin kashi 13.2 cikin 100 a bana, duk kuwa da annobar coronavirus da ake fama da ita.
Rahoton ya kuma nuna cewa bankunan kasuwanci na First Bank, UBA, GTBank, Access da kuma Zenith su ne suka tattara kaso mafi tsoka na Naira biliyan 18 da miliyan 400 daga irin kudaden harajin da suke cirewa daga asusun abokan huldarsu a watanni ukun farkon shekara ta 2020.
Abokan huldar sun koka
Da take tsokaci a kan lamarin, wata ma’aikaciyar gwamnati, Misis Victoria Chimezie, ta ce ba za ta iya kididdige sau nawa bankunan suka dibar mata kudade ba.
“Duk lokacin da aka turo min da kudi, ko da kuwa N1,000 ce, sai an cire min N50. Wannan abin takaici ne matuka”, inji ta.
Aminu Aliyu, wanda ke harkar kayan abinci a kasuwar Wuse da ke Abuja, ya koka da cewa baya ga kudaden da ake cire masa a kowacce hada-hada, wannan karon har a karshen wata ma bai tsira ba.
Shi kuwa Onyekachi Kelechi kira ya yi ga gwamnati da ta ceto ’yan Najeriya daga abin da ya kira damfarar da bankunan ke yi ko manufarta ta daina amfani da tsabar kudade ta yi nasara.
A nasa bangaren kuwa, Isaiah Osita cewa ya yi, “Tilas ta sa na rufe asusun ajiyata a daya daga cikin irin wadannan bankunan saboda abin da suke yankar min ya yi yawa”.
CBN ya kawo dauki
Ko a ’yan kwanakin nan dai sai da CBN ya kwato wasu kudade da yawansu ya kai kusan Naira biliyan 60 daga bankunan, wadanda aka yanka daga abokan hulda ba bisa ka’ida ba.
Mataimakiyar darakta a sashen kare hakkokin abokan hulda na bankin, Misis Chinyere Obilor, ta ce an tattara kudin ne daga korafe-korafe guda 13,000 da aka karba kan bakuna daban-daban game da cire kudin ba bisa ka’ida ba.
To sai dai masana na hasashen cewa matukar ba a dauki matakin da ya dace ba, akwai yiwuwar korafe-korafen su rubanya a watanni masu zuwa bisa la’akari da alkaluman Hukumar Kula da Had-hada Tsakanin Bankuna wadanda suka nuna cewa asusun ajiya guda miliyan 35 ne suka karu a kasar tsakanin watan Janairu zuwa 30 ga watan Mayun bana.
Hanyar kauce wa yawan yankar kudi
Wani ma’aikacin banki mai suna Joseph Enenche ya ce hanyar da mutum zai bi don takaita yawan yankar masa kudi daga bankunan ita ce ta takaita yawan cirewa ko saka kudin da yake yi da asusun.
“Abin da hakan ke nufi shi ne ba wanda zai yankar maka kudi idan ba ka saka ko cire kudi ko dai ta kai tsaye ko kuma ta amfani da intanet ba.
“Babu mahalukin da zai dibar maka kudi idan ba ka yi wata hada-hada da shi ba”, inji shi.
Shi kuwa wani shehin malami da ya kware a harkar kudi da kasuwar hannun jari a Jami’ar Jihar Nasarawa, Farfesa Uche Uwaleke, cewa ya yi, “Makasudin kafa bankunan kasuwanci shi ne don su rika bayar da rance.
“Sai dai abin takaici shi ne yanzu duk sun sauka daga layin sun kuma bige da cire kudi daga abokan huldarsu ba bisa ka’ida ba don su sami riba.
“Wannan ba abu ne mai dadi ba saboda ya yana yi wa kwastomominsu illa tare da dakile yunkurin daidaita harkar musayar kudade.
“Maganar gaskiya ita ce CBN ya fito da sabbin manufofi don kare hakkin masu ajiya da kuma hukunta bankunan da suka yi kunnen uwar-shegu. Na san bankin ya yi matukar kokari wajen kwato kudade da dama sakamakon hakan.
“Sai dai ina ba da shawara ga bankin da ya fi mayar da hankali wajen kare faruwar barnar fiye da hukunta wadanda suka karya dokar.
“Hakan ne kadai zai sa a yi wa tufkar hanci”, in ji Farfesa Uwaleke.
Inganta hanyoyin samun kudin shiga
Da ya ke nasa tsokacin, wani babban ma’aikacin banki da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce akwai cire kudaden da kwastomomi za su iya gujewa.
Ya bayar da misali da cewa mutum zai iya cewa ba ya bukatar a tura masa da sakon kar-ta-kwana idan ya yi wata hada-hada, sakon imel ma kawai ya wadatar, yana mai cewa hakan zai sa banki ba zai caji mutum ba a karshen wata.
Ya lura cewa yanzu haka ma akwai bankunan da ke kokarin amfani da manhajar aikawa da sako ta yanar gizi ta WhatsApp domin karbar irin wadannan sakonnin.
Ya kuma ce hanya daya tilo da bankunan za su inganta hanyoyin samun kudin shigarsu ba tare da cire kudin abokan huldarsu ba ita ce ta hanyar dawo da bayar da rance.
Ya kuma shawarce su da su kara zuba jari a harkar sadarwa domin kara yawan abokan huldarsu.