Yadda barawo ya saci mota da gawar tsoho a ciki
’Yan sandan a kasar Meziko sun kama wani da ake zargi da satar mota dauke da gawa, bayan ya sato motar ba tare da sanin akwai gawa a ciki ba. ’Yan sandan Tlakuepakue sun bayyana haka ne a shafinsu na Facebook, inda suka ce motar da aka sata an tanade ta ce da nufin daukar […]
’Yan sandan a kasar Meziko sun kama wani da ake zargi da satar mota dauke da gawa, bayan ya sato motar ba tare da sanin akwai gawa a ciki ba.
’Yan sandan Tlakuepakue sun bayyana haka ne a shafinsu na Facebook, inda suka ce motar da aka sata an tanade ta ce da nufin daukar gawar wani tsoho mai shekara 80 da ya rasu a asibitin garin Guadalajara don kai gawar makabarta a binne.
’Yan sandan sun ce, sun kama wanda ake zargin mai suna Annibal Saul N. mai shekara 40, wanda ya bayyana wa ’yan sandan cewa, shi ya dauki makullin motar da aka bari a sarari don haka ya yanke shawarar ya yi gaba da motar a daren Juma’ar da ta gabata.
Jami’an tsaro sun yi nasarar kama barawon motar ne bayan sanar da jami’an binciken motoci a manyan hanyoyi. ’Yan sandan sun ce, yanzu haka sun mika wanda ake zargi ga mahukunta don yanke masa hukuncin da ya dace.
A yanzu haka an karbo motar da gawar da aka sacen.