Yadda barayi suka addabi majinyata a asibitin Gombe
Matsalar dai ta sa ala tilas hukumar asibitin ta canja masu gadi.
Kananan barayi da suke sajewa da ’yan uwan majinyata a Asibitin Kwararru na Gombe sun addabi majinya ta da sace-sace.
Hakan dai ya sa tilas hukumar asibitin ta canja masu gadi.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 40 a kauyukan Zamfara
- Mukabala: Yau za a yi ta ta kare tsakanin Sheik Abduljabbar da malaman Kano
Koke ya yi yawa ne daga majinyata kan yadda ake yawan sace musu kudade da kayayyakin da ma magunguna.
Shugaban hukumar gudanarwar asibitin, Dokta Shu’aibu Mu’azu ya ce korafin ya same su kuma sun lashi takobin kawo karshen matsalar.
Dokta Mu’azu, ya ce suna kokari tsakanin su da jami’an tsaron asibitin wajen ganin sun kama bata-garin da suke musu satar don mika su ga ’yan sanda.
Ya kuma ce suna kokari wajen wayar da kan majinyata da suke ziyartar asibitin kan daukar matakan tsaro da kai rahoton motsin duk wanda basu yarda da shi ba ga jami’an tsaron da ke asibitin.
Daga nan sai Dokta Shu’aibu, ya ce sun rubuta korafi ga Ma’aikatar lafiya ta Jihar kan matsalar tsaron asibitin kuma tuni ta amince musu su canja kamfanin da ke samar da tsaron.
wasu majinya ta da suka zanta da Aminiya sun koka kan yadda suka ce bata-garin na shiga asibitin suna dauke musu kayayyakin amfani da magunguna.