Yadda barayi suka bugar da mu suka sace mana mota – Asnanic, Kamal
A ranar Larabar makon jiya ce fitaccen mawaki Nazifi Asnanic da Darakta Kamal S. Alkali suka fada hannun barayi a Abuja inda bayan sun sanya musu gubar da ta bugar da su suka sace musu mota da kudi da wayoyi da kuma na’urar laptop.Aminiya ta tuntubi mawakin ya kuma yi bayanin yadda al’amarin ya faru […]

A ranar Larabar makon jiya ce fitaccen mawaki Nazifi Asnanic da Darakta Kamal S. Alkali suka fada hannun barayi a Abuja inda bayan sun sanya musu gubar da ta bugar da su suka sace musu mota da kudi da wayoyi da kuma na’urar laptop.
Aminiya ta tuntubi mawakin ya kuma yi bayanin yadda al’amarin ya faru inda ya ce: “A ranar Talata (ta makon jiya) sai wani mutum mai suna KB ya kira ni a waya bayan ya yi mini bayani ko shi wane ne na gane shi, na taba haduwa da shi a dakin wani abokina a lokacin da na je Ummara. Bayan mun dawo gida sai wata rana ya kira ni a waya ya ce akwai wakar da yake so na yi masa, wato wata Sanata ce a Jihar Taraba take so a yi mata waka kuma a cewarsa ta ce ni ne zan yi mata wakar. A nan ne ma yake gaya mini ya samu lambar wayata ne a wurin makadi Alee Baba. Sai ya tambaye ni yadda za a yi sai na ce su aiko mini da bayanin abin da suke so a yi musu waka a kai, ni kuma zan ga yadda aikin zai kasance. Amma sai KB ya ce matar ta ce tana so ta gan ni ne. “ Inji Nazifi.
Ya ce, da farko ya nemi ya ki zuwa Abuja saboda yawan aikin da yake gabansa, amma da yake tsautsayi ba ya wuce ranarsa kuma KB ya yi masa dadin baki cewa harkar sana’ata ce bai kamata ya yi wasa da ita ba, sai ya amsa gayyatar. A lokacin sai ya sanar da matarsa wata kila gobe (Larabar makon jiya) zai tafi Abuja. Daga nan ya fara neman yadda zai yi tafiyar kasancewar bai yi wa motarsa juyen bakin mai ba, da har ya yi tunanin daukar motar Kwankwasiyya, sai ya tuna abokinsa Kamal S. Alkali ya gaya masa cewa zai je Abuja, sai ya kira shi ya gaya masa cewa za su tafi tare. “Washegari muka tafi a motar Kamal baka kirar Honda. Muka same shi a Elith Soth Hotel da ke Gwagwalada. Yana fitowa na gane shi. A nan dai ya kai mu dakin da yake a hotel din wanda muka ga har da kayansa a ciki. Bayan mun yi sallah sai ya tambaye mu irin abincin da muke so, muka ce akwai shinkafa sai aka gaya mana sai sakwara. Bayan an kawo mana sakwarar sai ya kawo mana lemon kwali na Fibe Alibe ya zuzzuba mana a kofuna. Tun da muka gama cin abincin nan sai na ji kaina ya yi min nauyi har nake gaya musu halin da nake ciki, sai KB din ya ce ko dai gajiyar hanya ce. Daga wannan maganar da na yi ba mu sake sanin halin da muke ciki ba sai da muka yi kwana uku a haka, inda na tsinci kaina a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada, a can Abuja. Ashe ba mu sani ba KB ya zuba wani abu a cikin lemon da ya kawo mana wanda ya sa daga ni har abokin nawa muka yi ta barci ba kakkautawa.” Inji shi.
Daga baya ya kwashe musu Naira dubu 40 da wayoyi hudu da kuma bakar motar Kamal kirar Honda.
“Da ma tun da muka shiga Abuja na kira wani abokina da yake zaune a can na tambaye shi hanyar da za a je Gwagwalada duk da cewar ban gaya masa ni ne zan je ba, inda na gaya masa cewa abokina yake son zuwa, na yi hakan ne don ina so na kai masa ziyarar bazata idan na gama abin da na je yi Abuja. Bayan mun yi kwana biyu ba a san inda muke ba sai Aminu Saira ya buga wa wannan abokin nawa ya tambaye shi cewa mun shigo Abuja tun ranar Laraba amma ba a samun mu a waya, don haka yana son ya bincika masa halin da muke ciki. A nan ya sanar da shi bai san na je Abuja ba, sai dai kawai ya san na kira shi na tambaye shi cewa abokina na son sanin hanyar zuwa Gwagwalada. A takaice dai ana wannan abokin nawa ya tafi Gwagwalada ya rika bincike har ya hadu da mu a asibitin.” Inji shi.
Wakilinmu ya tuntubi Darakta Kamal S. Alkali inda ya ce ya bar wa Allah komai, domin Shi ne zai mayar masa da mafi alherin abin da ya rasa.
Wakilinmu ya je Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Gwagwalada inda wata jami’a da ke sashin Agajin gaggawa ta tabbatar da kawo su Nazifi, sun gano an sa musu guba a cikin abinci, amma ta ce a ranar da aka kawo su aka sallame su.
Da wakilinmu ya tuntubi Babbar Jami’ar Hulda da jama’a ta ‘yan sandan Abuja ASP Hyelira Altine Daniel ta tabbatar da aukuwar lamarin.
A yanzu dai suna ci gaba da jinya a gidajensu da ke Kano.