Yadda barayi suka shammaci wakilinmu a Legas

Mutane za su yi mamakin abin da ya faru gare ni da har ta kai na ce ba zan sake karanta jarida ba a cikin motar haya. Ba komai ya sa na yanke shawarar haka ba sai don irin satar da aka yi mani ta rainin hankali a cikin motar hayar da na shiga daga […]

Yadda barayi suka shammaci wakilinmu a Legas
Yadda barayi suka shammaci wakilinmu a Legas

Mutane za su yi mamakin abin da ya faru gare ni da har ta kai na ce ba zan sake karanta jarida ba a cikin motar haya. Ba komai ya sa na yanke shawarar haka ba sai don irin satar da aka yi mani ta rainin hankali a cikin motar hayar da na shiga daga tashar motar da ake kira First Gate da ke
Ikeja zuwa tashar motar da ke unguwar Ojota a Jihar Legas a makon da ya gabata.
Tun da nake aiki a Jihar Legas Allah Ya kare ni, ban taba haduwa da barayi ko ’yan fashi ba saboda ba a taba yi mani sata a gidana ko wurin aikina ba. Duk kokarin da kananan barayi suka rika yi na shiga ta taga ko kofar dakina, Allah bai ba su iko ba, sai a karon banza wasu gungun ’yan sane da muka shiga mota tare da su suka fake ni, suka dauke mani kananan na’urorin da nake yin aikin jarida da su.
Ba dauke na’urar daukar magana ko ta daukar hoto ce ta fi ba ni takaici ba sai irin sa’ar da suka samu a kaina har suka sace mani abin da da na sanya a cikin aljihuna. Kodayake masu iya magana sun ce maso abin ka ya fi ka dabara amma ni na tabbatar har ga Allah jarabawa ce daga Allah, domin duk matakan da suka kamata na kula da abin da da ke cikin aljihuna na dauka don ganin ba su salwanta ba.
Na farko, na yi addu’a kafin na shiga motar. Na biyu, na sanya su a cikin wata karamar jaka, sannan na saka a cikin aljihuna. Na uku, muna tafiya ina taba aljihuna lokaci zuwa lokaci amma duk da haka an ce kaddara ta riga fata, sai da suka san yadda suka yi suka dauke na’urorin.
Yadda lamarin ya auku shi ne, na fito aiki da safiyar ranar Laraba, ina zuwa ofis sai daya daga cikin wadanda suke sanar da ni abin da yake faruwa a yankin Mil 12 ya kira ni a waya, ya sanar da ni cewa yana son ganina akwai labari. Nan da nan na dauki kayan aikina, wato rediyo da na’urar kyamara na nufi tashar First Gate don shiga motar zuwa unguwar Ojota; inda daga nan zan shiga wata motar don zuwa Mil 12. Da farko dai mun shiga motar Ojota da kokawa amma duk da haka ina kula da aljihunana, inda na sanya kudina da kuma inda na sanya kayan aikina.
Bayan mun shiga mun fara tafiya sai na fara karanta jaridar Daily Trust da ke hannuna, inda rubutun Muhammed Haruna na bayan jaridar ya ja hankalina. Ina karanta jaridar ina kula da alajihuna saboda yadda na san halin ’yan sane a Legas. Ina cikin karatun sai wani sakin layi na rubutun ya ja hankalina, daidai inda Muhammed Haruna yake magana a kan martanin da Shugaba Jonathan ya mayar wa gwamnonin Arewa a kan Boko Haram. Ashe mutumin da ya zauna a kusa da ni ya riga ya dauke na’urorin da ke cikin aljihuna, da ya lura hankalina ya karkata kan karatun jaridar. Nan da nan sai ya ce zai sauka, ni kuma Allah bai sa na sake taba aljihuna ba. Har ya sauka hankalina bai ba ni ya yi mani sata ba sai da muka zo tashar Ojota, inda kowa da kowa zai sauka. Sai kawai na taba aljihuna, na ga ba komai. Na ce wa yaron motar da direbansa su tsaya na duba cikin motar ko na yar da kayana. Suka dan dakata na duba karkashin kujerun amma ban ga komai ba. Su ma suka tabbatar mani cewa ba abin da na yar a cikin motarsu.
Nan take na fara Istirja’i da neman taimakon Ubangiji. Haka na ci gaba da tafiya cikin bakin ciki har na je na dawo ofis ina mamakin yadda al’amarin ya auku da irin tsautsayin da ya fada mani. Daga bisani sai na ci gaba da addu’ar Allah Ya kare ni, Ya dora ni a kan duk wani mugu, Ya hada ni da alherin da ke cikin Legas, Ya kare ni da sharrin da ke cikin jihar.Wannan ya zama darasi a gare ni.
Haruna, wakilin Aminiya ne a Legas, za a iya tuntubarsa a (08027406827), ko ta I-mel: [email protected] ko [email protected]