Yadda barayin mutane suka addabi mutanen yankin Rigasa
Mazauna yankin Rigasa da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna na ci gaba da kokawa kan yadda masu garkuwa da mutane suka addabe su a ’yan watannin nan inda suke hana su barci da kwanciyar hankali. Masu garkuwa da mutanen kan shiga yankunan ne a duk lokacin da suka ga dama musamman da daddare […]
Mazauna yankin Rigasa da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna na ci gaba da kokawa kan yadda masu garkuwa da mutane suka addabe su a ’yan watannin nan inda suke hana su barci da kwanciyar hankali.
Masu garkuwa da mutanen kan shiga yankunan ne a duk lokacin da suka ga dama musamman da daddare su dauki duk wanda suke so ba tare da fuskantar wani kalubale ba.
Binciken da Aminiya ta yi ya gano cewa karar bindiga ya zama ruwan dare ga mutanen yankin, inda hakan ke hana su barci. Yankunan da abin ya kamari sun hada da Ado Gwaram da Nariya da Kwate da Tudun Barde da Tudun Ladi Wudil da Mai Giginya da sauran yankunan da ke tsallaken titin jirgin kasa da ke Rigasa.
Lalacewar tsaro a yankunan ta tilasta wa wadansu daga cikin mazauna yankin yin zanga-zanga domin nuna bacin ransu tare da yin kira ga wakilan Majalisar Dokokin Jihar su sa a kai musu dauki. Zanga-zangar an yi ta ce a karkashin jagorancin Barista Shehu Sani Surajo.
Wakilinmu wanda ya ziyarci Unguwar Rigasa ya gano cewa wadansu daga cikin mazauna unguwar na cikin damuwa domin rashin sanin wanda za a sace nan gaba. Kuma akasarin wadanda ake sacewa talakawa ne.
Mohammed Abdullahi, wani matashi da aka sace shi a watan jiya a hanyarsa ta zuwa gona kuma wadanda suka kama shi suka bukaci kudin fansa Naira miliyan 15 a karshe bayan ciniki sun amince su karbi Naira dubu 350.
Bayan dan uwansa mai suna Usman ya kai musu kudin, sai shi ma suka rike shi cewa sai an kara musu Naira miliyan 10. A yanzu haka iyalansu sun sake amincewa su kara Naira miliyan daya da wayar hannu kirar Tecno ta Naira dubu shida kamar yadda barayin mutanen suka bukata.
Aminiya ta samu labarin wani matashi dan kimanin shekara 23 mai suna Musa wanda aka tsinci gawarsa a Tudun Barde bayan an sace shi kuma mahaifinsa ya biya Naira dubu 50. An ce bayan sace shi sun kira suna bukatar Naira dubu 750 amma da suka fahimci ’yan uwansa ba masu kudi ba ne sai suka ce a kai masu dubu 50, bayan an kai musu sai bayan kwana biyu aka tsinci gawarsa a wani kango.
Yusuf Isa da kwanan nan aka sako matarsa mai dauke da cikin wata takwas, ya ce “Sun dauke ta ce a watan jiya lokacin da suka shigo gidanmu. Tana da cikin wata takwas bayan sun tafi da ita sai suka bukaci a ba su Naira miliyan biyar wanda kuma ba ni da su. Mutanen unguwa ne suka hada wasu ’yan kudi aka kai musu kafin suka sako ta.
Gaskiyar magana idan da gaske wannan gwamnati ta talakawa ce to akwai bukatar ta kawo karshen wannan rashin tsaro da ya addabi mutane ba ma a Rigasa kadai ba a jihar da kasa baki daya,” inji shi.
Yusuf Ishak ya yi bayanin yadda ya sha wahala a hannun masu garkuwa da mutanen lokacin da ya kai musu kudin fansar da suka nema kafin su saki wani abokinsa da suka sace a watan Satumba.
“Wani abokina suka sace suka ce a ba su wasu miliyoyin Naira amma daga baya sai suka amince su karbi Naira dubu 350. Sai na amince zan kai musu kudin a can dajin Gurguzu. Na bar gida karfe biyar na yamma muna ta magana da su ta waya suna sake nanata cewa in zo ni kadai. Daga baya sai suka kira ni cewa sun ga wani mai babur ya ajiye ni. Na ce musu dan acabar da ya kawo ni ne,” inji shi.
Ya ce “Sai daga baya na hango wani mutum sanye da kayan sojoji ya daga min hannu. Da na karasa wajen shi sai ya tambaye ni ko kudin sun cika na ce sun cika, daga nan sai wadansu abokansa suka fito da makamai. Abin da kawai zan iya tunawa ke nan sai kawai bude ido na yi na ji ni a daure sannan kuma sun rufe min ido da kyalle. Sai suka shaida min wai kudin da na kawo dubu 350 sun yi kadan, don haka sai na kara musu Naira dubu 650. Kusan dai miliyan daya aka kashe kafin suka sako mu.”
Shi kuwa Mohammed Sa’id godiya ya yi ga Allah da Ya taimake shi ya tsira daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi. “Sun zo da nufin daukar matata ce amma da na ki sai suka ce in bi su mu tafi, na kuma bi su tare da ci gaba da yin addu’o’i a kan hanya. Amma fa sai da suka karbi Naira dubu 36 da suka gani cikin dakina. Mun yi tafiyar wajen sa’a uku a cikin daji, bayan mun isa sansaninsu sai suka kira mahaifina wanda ya yi musu magana da Fulatanci.
“Suka bukaci a ba su Naira miliyan 20 shi kuma mahaifina ya fada musu cewa bai da wannan kudi amma zai iya ba su Naira dubu dari. Sai suka zage shi tare da fada masa cewa su fa babu ruwansu da kasancewarsa Bafulatani domin kudi kawai suke nema. Bayan kwana biyu sai wanda aka bari yana gadina barci ya kwashe shi daga nan Allah Ya taimake ni na gudu,” inji shi.
Ita kuwa Fatima ’ya’ya uku aka sace mata kuma da mijinta ya kai kudin fansarsu sai shi ma suka rike shi. A cewarta ba ta nan ranar da suka je gidansu kuma sun kwashe Naira dubu 450 a dakinta.
Ta ce sun yi kwana goma suna tattaunawa da su kafin su amince a kai musu Naira dubu 450 da katin waya na Naira dubu 30. “Mijina ya amince zai kai musu kudin da ya je sai shi ma suka rike shi har sai da muka kara musu Naira dubu 700 da katin Naira dubu 30. Akalla dai sai da muka kashe kusan Naira miliyan daya da rabi kafin aka sako su,” inji ta.
Malam Dahiru an sace shi ne a gonarsa a watan Satumba sannan aka sako shi bayan kwana uku. “Sun karbi Naira dubu 300 sannan suka kwace babur dina da na wanda ya je kai musu kudin. A yanzu haka ban gama biyan kudin da na amsa bashi ba, sannan ga babur ban biya ba. Haka kuma ban koma ganar ba saboda mutane na tsoron shiga gonakinsu duk kuwa da cewa amfanin gonar ya isa girbi,” inji shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo ya ce an kara tsaurara tsaro a yankin Rigasa da Nariya da kewaye domin a kwanakin baya rundunar ta yi nasarar kai samame kan barayin har ta kwato mutum takwas.
Ya ce bayan haka Kwamishinan ’Yan sandan Jihar da Gwamnan Jihar sun tattaunawa da mazauna yankin Nariya domin sanin yadda za a inganta tsaro.
Ya kara da cewa rundunar ta kara yawan ’yan sanda masu sintiri a yankunan Rigasa, gwamnatin jihar kuma ta tattauna da rundunar sojoji domin ganin yadda za a inganta tsaro a yankin.
DSP Sabo ya ce a yanzu akwai jami’an tsaro na hadin gwiwar sojoji da ’yan sanda da ke aiki a yankin Nariya da Rigasa domin dakile ayyukan ta’addanci.